Janar Attahiru ya zama shugaban soji na biyu da ya mutu a hadarin jirgi


Juma'ar yau bata yiwa yan Najeriya dadi ba yayinda shugaban hafsoshin Sojin kasan Najeriya, Laftanan Janar Ibrahim Attahiru, ya mutu tare da wasu manyan hafsoshi a hadarin jirgin saman.

Duk da cewa ba'a samu cikakken bayanin abinda ya faru har yanzu ba, hukumar Sojin saman Najeriya ta tabbatar da faruwar wannan hadari .

Janar Attahiru ne mutum na biyu da ya mutu kan wannan kujera sakamakon hadarin jirgi.

Na farko shine Laftanan Kanar Joseph Akahan wanda shine shugaban hafsoshin Soji tsaknain Mayun 1967 da Mayun 1968 lokacin da ya mutu a hadarin jirgi mai saukar angulu lokacin yakin basasa.

Akahan wanda dan asalin garin Gboko a jihar Benue ne na cikin wadanda suka yiwa Janar Aguyi Ironsi juyin mulki suka dankawa Yakubu Gowon mulki.

An nada shi shugaban hafsoshin Soji ne ana gab da fara yakin basasa.

Lokacin da ya mutu a hadarin jirgin, an maye gurbinsa da Janar Hassan Katsina.

Karo uku kenan a wannan shekarar da jirgin sojin Najeriya zai samu hadari kuma ayi rashin rayukan hafsoshi.

A ranar Lahadi, 21 ga watan Febrairu, jami'an hukumar mayakan sama bakwai sun rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin Beechcraft KingAir B350i da ya fado a Abuja.

Hakazalika, a ranar Laraba, 31 ga Maris, 2021, jirgin yakin sojin Najeriya Alpha-Jet wanda ke artabu da yan ta'addan Boko Haram ya samu matsala a sararin samaniya kuma yayi hadari.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN