Laftana Janar Ibrahim Attahiru tsohon shugaban sojin kasa na Najeriya tare da wasu Brigediya Janar guda 3, Manjo 2 da sauran hafsoshi sun mutu a hatsari da jirgi kirar Beechcraft Air 350 ya yi a filin sauka da tashin Jiragen sama na Kaduna ranar Juma'a da karfe 6:45 na yamma lokacin da ake ruwan sama.
Shafin labarai na ISYAKU.COM ya samo cewa Jirgin Beechcraft Air 350 kirar kasar Amurka ne wanda aka kera domin dalilan amfanin soji, musamman lokacin yakin Duniya na biyu.
Jirgin yana daukan fasinja 9 bayan matuka jirgin da masu hidama a ciki.
Kazalika jirgin yana gudun kilomita 568 kph a cikin awa daya a sararin samaniya. Kuma zai iya tafiya har tsawon kilomita 3092 a zango daya. Haka kuma Masana sun ce jirgin baya shan mai sosai.
Reported by ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari