Hotuna: Yansanda sun sheke yan fashi 2 da mace 1 sun kama tarin makamai a jihar kudu


Rundunar yansandan jihar Ebonyi ta sheke wasu mutum biyu da mace daya daga cikin gungun Yan fashi da makami da suka farmakin wani Banki a Onueke ranar Talata

.Kakakin rundunar yansandan Najeriya Frank Nba ya tabbatar da haka a takarda da ya fitar wa manema labarai. Ya ce yansanda sun kashe mutanen biyu tare da wata mata da ke tare da su yayin musanyar wuta da bindigogi. Sakamakon haka yansanda sun kama bindigogi guda 2 kirar AK47 da albarussai masu yawa.

Mba ya ce rundunar yansandan jihar ta kama tarin makamai da albarussai da aka yi satar shiga da su jihar Ebonyi tare da damke wasu mutane dangane da lamarin.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN