Hisbah ta kori babban jami'inta da aka kama tare da matar aure a dakin Otal a Kano


Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kori wani babban jami'inta bayan zargin kama shi tare da wata matar aure a wani dakin Otal a Unguwar Sabon Gari da ke Kano.

An kama jami'in mai suna Sani Rano a yanayi da ya haifar da zargi a dakin Otal tare da wata mata ranar Talata 16 ga watan Fabrairu 2021.

Sai dai a wata hira da SaharaReporters jami'in sadarwa na hukumar Nabahan Usman ranar Talata 10 ga watan Maris, ya ce jami'in da ake zargi baya da laifi, domin matar da aka same shi tare da ita a dakin wannan Otal diyarshi ce.

Sai dai Kakakin hukumar Hisbah na jihar Kano Lawal Fagge ya tabbatar wa Jaridar Vanguard da korar babban jami'in hukumar da ake cece kuce a kansa ranar Talata 4 ga watan Mayu.

Rahotanni sun ce hukumar ta dauki matakin korar jami'in ne bisa shawarar rahotun Kwamiti da hukumar ta kafa domin binciken lamarin.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN