Hatsarin jirgin ruwan Kebbi: An gano gawawwaki 76 kawo yanzu


Hukumar kula da hanyoyin ruwa ta Najeriya (NIWA) ta ce kawo yanzu an gano gawarwaki 76 daga hatsarin jirgin ruwan da ya faru a kauyen Tshohuwar Labata da ke karamar hukumar Ngaski a jihar Kebbi.

Manajan NIWA a jihar, Birma Yusuf, ne ya bayyana hakan ga jaridar Daily Trust a ranar Juma’a, inda ya ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da binciken saboda ana sa ran za a gano sauran gawarwakin.

Gawarwakin da aka gano sun yi ta yawo a gabar Kogin Neja kusa da inda mummunan hatsarin ya auku.

Yusuf ya koka kan rashin isasshen kayan aikin hukumar don aikin ceto.

Ya ce hukumar na da kwarewar aikin ceto sannan ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kebbi da ta taimaka wa hukumar da jiragen ruwan domin inganta ayyukan su.

"Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 76. A koyaushe muna zargin masu gudanar da kwalekwale da yin lodin da ya zarta kima da kuma amfani da tsofaffin jiragen ruwa."

Zuwa daren Juma’a masu aikin ceto sun yi nasarar ceto kimanin mutum 30 da ransu daga cikin fasinjoji jirgin.

Suleman Bobo daya daga cikin masu aikin kuma Shugaban matasa garin Warra ya tabbatar wa da wakilin jaridar Aminiya.

Tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinja 160 ya kife a kogin Niger ta Kebbi

Da farko Legit.ng ta kawo cewa Fasinjoji masu tarin yawa sun nitse a yankin arewa maso yammacin Najeriya a ranar Laraba bayan tafkeken jirgin ruwa dauke da fasinja 160 ya kife a kogin Neja, jami'i mazaunin yankin ya tabbatar.

Jirgin ruwa da ya bar jihar Kebbi yana tunkarar yankin arewa maso yammacin jihar Kebbi ya fashe sannan ya nitse, Abdullahi Buhari Wara, hakimin Ngaski ya tabbatar.

Tunidai masu ceto suka fada kogin amma mutum 22 tare da gawar mutum daya suka iya tsamowa, Wara yace a yanzu kusan fasinjoji 140 ne babu duriyarsu.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN