Hukumar kula da makarantun frimare ta jiha, SUBEB, ta jihar Niger ta kori malaman makarantun frimare 20 a sassan jihar daga aiki saboda satifiket ɗin bogi da rashin zuwa aiki.
A cewar kamfanin dillancin labarai, NAN, an sanar da korar su ne cikin wata sanarwa da Idris Kolo, kakakin SUBEB, ya fitar a ranar Litinin kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Idris Adamu, Shugaban SUBEB na Niger, ya ce an kori malamai huɗu daga Gbako, sai uku-uku daga Bida da Lapai.
Ya kuma ce an sallami biyu daga aiki a ƙananan hukumomin Agaie, Katcha da Lavun yayin da aka sallami mutum ɗai-ɗai a ƙananan hukumomin Mashegu, Munya da Shiroro. Ya kuma ce an kori malami ɗaya a Kontagora saboda rashin zuwa aiki.
"Hukumar ta yanke shawarar korar dukkan malaman da ba su cancanta ba a makarantun frimare a matsayin wani mataki na inganta koyarwa da karantarwa a makarantun frimare na jihar," in ji shi.
Shugaban na SUBEB ya ce hukumar tana mataki na farko na tantance ma'aikata ne kuma za ta cigaba da fatattakar ɓara-gurbi daga cikin ma'aikatan.
Source: Legit.ng News
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari