Fusatacciyar mata ta sanya maciji a cikin akwatin gawar mijinta don yin maganin wadanda suka kashe shi


An ga wata mata 'yar kabilar Ashanti wacce ta fusata game da mutuwar mijinta tana sanya maciji a cikin akwatin gawarsa domin ya yi maganin duk wanda ke da hannu a mutuwarsa.

A cikin faifan bidiyan da ake yadawa a shafukan sada zumunta, an ga matar zagaye da wasu daga cikin danginta da masu alhini wadanda suka zo don ta’aziyyar mamacin.

Sautin bayan fage ya ce macijin ya harbi harshen marigayin har sai da ya mutu, wannan ne ya sa matar ta ga ya dace ta binne shi tare da abin da ya kashe shi.

Kalli bidiyon a kasa:

Sai dai, da yawa waɗanda suka san al'adar sun bayyana cewa wannan don yin maganin duk wanda ke da alaƙa da mutuwar mamacin ne.

Misali, funghana_ ya ce:

"An yi amannar cewa mutumin bai yi mutuwar Allah ba, don haka ruhun macijin zai sari duk wanda yake da hannu a cikin mutuwarsa da zaran macijin ya mutu."

Bayan ta yi wasu yan surkulle, sai matar ta dauki macijin da ke rataye a wuyanta ta saukar da shi cikin akwatin yayin da take nuna alamun da ke nufin "ka yi maganinsu ba tare da tausayi ba".

A wani labarin, iftila'in ya faru ne a karshen mako a jihar Neja, biyo bayan hatsarin jirgin ruwan da ya faru a garin Tijana na karamar hukumar Munya da ke jihar wanda ya kai ga mutuwar mazauna kauye sama da 15 a cikin jirgin ruwan a cikin wani kogi da ke yankin.

Jirgin ruwan ya kife ne da misalin karfe 6:00 na yamma a ranar Asabar lokacin da ake zargin mazauna kauyen sun dawo daga wata kasuwar yankin da ke Zumba a karamar hukumar Shiroro ta jihar.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN