Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa kotu, sun yi awon gaba da alkali a Katsina


Yan bindiga sun yi garkuwa da alkali a cikin kotun Sharia dake kauyen Bauren Zakat a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Kamar yadda ganau suka sanar da Daily Trust, maharan sun balle kotun inda suka shiga wurin karfe 3 na yammacin ranar Talata kuma suka yi awon gaba da alkalin mai suna Alhaji Husaini Sama'ila.

An mayar da kotun shari'ar ne karamar hukumar Safana saboda dalilan tsaro.

Har yanzu dai ba a san dalilin da ya kai alkalin kotu ba duk da yajin aikin da kungiyar ma'aikatan shari'a na Najeriya (JUSUN) ke ciki.

Katsina tana daya daga cikin jihohin yankin arewa maso yamma da 'yan bindiga suke cin karensu babu babbaka.

Har a halin yanzu jami'an tsaro basu yi martani kan aukuwar lamarin ba.

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito cewa ma’aikatan shari’a sun shiga yajin-aiki, har an kai ga rufe kotu da-dama a Najeriya.

Shugaban kungiyar malaman shari’a na bangaren jihar Legas, Kehinde Shobowale Rahamon, ya bayyana abin da ya sa ma’aikatan su ka tafi yajin-aiki.

Mista Kehinde Shobowale Rahamon ya ce har yanzu doka ta 10 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kai ba ta fara aiki ba har yanzu.

A wani labari na daban, Dino Melaye, tsohon sanatan da ya taba wakiltar Kogi ta yamma, yace shugaban kasa Muhammadu koyaushe baya nan kuma bashi da lokaci.

Jigon jam'iyyar PDP yace ba zai yuwu shugaban kasan ya ki yi wa kowa magana ba sai ta bakin masu magana da yawunsa, TheCable ta wallafa.

Ya ce shirun Buhari na da matukar illa ga yaki da rashin tsaro a kasar nan. Melaye ya sanar da hakan ne a yayin tattaunawar da aka yi da shi a AIT ranar Juma'a.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN