Da duminsa: An sheke jami'an 'yan sanda 6 yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki ofishin 'yan sanda


Yan bindiga da ake zargin mambobin IPOB ne sun kai mugun farmaki ofishin 'yan sanda dake Odoro Ikpe a karamar hukumar Ini ta jihar Akwa Ibom.

Jami'ai shida sun rasa rayukansu a harin da aka kai a sa'o'in farko na ranar Asabar, 8 ga watan Mayu, The Punch ta ruwaito haka.

Hakazalika, a yayin bada rahoton harin, The Cable ta ce wannan ne karo na biyu da ake kai hari cikin mako daya a jihar ta kudu.

Legit.ng ta tabbatar da cewa wannan harin ya zo ne yayin da ake ta kai hare-hare ofishin 'yan sanda a yankin.

Hare-haren 'yan bindiga ya zama ruwan dare domin kuwa ba a yin kwanaki kalilan ba tare da sun kai mugun hari ba. Suna kone ofishin 'yan sanda tare da kashe jami'ai.

Duk da ana zargin mambobin IPOB da kai miyagun hare-hare, su kan musanta hakan.

A wani labari na daban, kasa da sa'o'i 24 da nada sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Anambra, Christopher Adetokumbo Owolabi, 'yan bindiga sun kai farmaki ofishin 'yan sanda dake Obosi a karamar hukumar Idemili a jihar inda suka sheke 'yan sanda biyu.

'Yan bindigan sun kai farmaki ofishin 'yan sandan a yammacin Laraba inda suka saki dukkan masu laifi dake ofishin sannan suka banka masa wuta, Daily Trust ta wallafa.

Wata majiya mai kusanci da ofishin 'yan sandan tace 'yan bindiga sun isa da yawansu kuma sun kai hari ofishin wurin karfe 11 na dare. Ya bayyana sunayen jami'an da Sifeta James da Awalu.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN