Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba a daren Alhamis, 6 ga Mayu, sun yi yunkurin kai hari Hedikwatar’ Yan sanda ta Orlu a jihar Imo.
Jami'an tsaro a wani aikin hadin gwiwa, sun dakile harin kuma sun kashe akalla mutane takwas daga cikin maharan, jaridar The Punch ta ruwaito.
Legit.ng ta tattaro cewa sun kuma kwato motoci bakwai da maharan suka shigo domin ta’asar.
An tattaro cewa an shafe tsawon awanni ana musayar wuta tsakanin ‘yan bindigar da jami’an tsaron.
Artabun ya haifar da firgici yayin da mutane suka rarrabu don kare kansu lamarin da ya sa hanyoyin da ke cikin garin Orlu da kewayensa zama tsit.
Da take bayar da rahoton faruwar lamarin, jaridar The Nation ta bayyana cewa ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ba amma wani babban dan sanda da ba a ambaci sunansa ba ya tabbatar da ci gaban.
An rahoto cewa babban jami’in dan sandan ya ce an tafi da gawarwakin ‘yan fashin da motocin zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sanda da ke Owerri.
Ya bayyana cewa ba a kona hedkwatar rundunar 'yan sanda ba kuma ba a kashe kowani jami'in tsaro a harin ba.
A gefe guda, ana fargabar mutane biyu sun rasa rayukansu bayan wasu mutane dauke da makamai sun kai hari kan motar banki a kauyen Elemosho da ke kan babbar hanyar Akure-Ondo a karamar hukumar Ondo ta Gabas ta Ondo da yammacin ranar Alhamis.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce ‘yan bindigan sun zo ne a cikin wata motar Lexus, kuma suka afka wa motar da ke kan hanyar zuwa Akure da misalin karfe 5 na yamma sannan suka yi awon gaba da wasu kudade da ba a bayyana yawansu ba.
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari