Da Dumi-Dumi: ISWAP Sun Afkawa Mafakar Boko Haram, Ana Kyautata Zaton Shekau Ya Mutu


Wasu da ake zargin 'yan ISWAP ne a ranar Laraba sun kashe shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, yayin wani kazamin fada a maboyar su ta Dajin Sambisa. In ji wata majiya da ba a tabbatar ba, Vanguard ta ruwaito.

Gandun dajin Sambisa yana da iyaka da kananan hukumomin Konduga, Bama, Gwoza Askira Uba, Hawul, Kaga da Biu a kananan hukumomin Borno, tare da wasu yankuna na Gujuba, Buni Yadi, Goniri a Yobe da Madagali a jihar Adamawa.

Wasu majiyoyi sun ce daruruwan mayakan ISWAP sun mamaye Sambisa da motoci dauke da manyan bindigogi da ke farautar Shekau wanda shi ne shugaban kungiyar Boko Haram.

Haka kuma an bayyana cewa ba kungiyar ISWAP ba ce ta kashe Shekau kai tsaye, ana zargin ya tarwatsa kansa ya kashe kansa ne a lokacin da ISWAP ta yi yunkurin cafke shi (Shekau) da ransa, a yayin musayar wuta.

Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance ko tabbaci kan mutuwar shugaban ‘yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo, jami’an tsaron Najeriya, mutane da yawa sun shiga dandalin su na sada zumunta na murnar mutuwar Shekau da safiyar Alhamis.

A cewar wani rahoton tsaro da aka samu ya ce, “majiyar da ba a tabbatar ba ta ruwaito cewa shugaban kungiyar JAS Abubakar shekau ISWAP ta hanbarar da mulkinsa kuma sun mamaye dajin sambisa baki daya.

“Tare da wadannan ci gaban ISWAP sun fi JAS kayan aiki da kudade. Don haka yanayin barnarsu zai canza, kuma akwai yiwuwar za a fuskanci hare-hare akai-akai a kewayen Konduga, Bama, Gwoza, Biu LGA’S da wani yanki na Adamawa.

"Duk 'yan Adam da ke kusa da wannan yankin su kasance masu lura da tsaro kuma su kasance masu sanya ido."

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN