-->

Ads

Burina shine in auri mata 20 - Mutumin da ya auri mata 12 ya haifar da cece-kuce a sabon bidiyo

Burina shine in auri mata 20 - Mutumin da ya auri mata 12 ya haifar da cece-kuce a sabon bidiyo


Wani magidanci ya bayyana cewa babban burinsa shine ya kara auren wasu matan duk da cewa tuni yana da 12.

Mutumin da ba a san kowanene ba, wanda ke alfahari da auren mata fiye da daya, a cikin wani bidiyo da @kingtundeednut ya wallafa a shafin Instagram, ya ce ya fara ne da mata daya amma ya yi la’akari da auren mata fiye da daya bayan ya samu wadatar dukiya.

Uwargidarsa da suka zauna tare tsawon shekaru 16 ta bayyana shi a matsayin mutum mai nuna kauna da kulawa. Ta ce ta yi mamaki ranar da ya sanar da ita shawarar da ya yanke na kawo wata matar amma ta yarda.

Abin sha'awa, yawanci yakan gaya wa sabbin matan a lokacin da ya kawo su cewa ya riga ya auri wasu matan, kuma galibi ba su da matsala da hakan.

A cikin irin wannan yanayin, yawancin mata sun rataya shawarar su na ci gaba da auren shi saboda ƙaunar da suke masa.

Mutumin da ya fara sana'ar gyaran takalmi kafin ya zama mai maganin gargajiya na daya a kasar ya ce yana da karfin ruhi da zai tabbatar da duk matar da ta gudu ta dawo.

Mai mata da yawan wanda bai damu da ra'ayoyin mutane game da shi ba yana zaune cikin farin ciki tare da matan a gida daya.

Mutane sun tofa albarkacin bakunansu kan bidiyon.

@anitajoseph8 ta yi martani:

"Suna jin muryoyi sannan kuma sai su dawo..ya sa su dawowa ahhhh inukwa nu me ehhhh."

@ladi64297 yayi sharhi:

"Wannan isasshen hanyar kamuwa da cuta ne faaaa daga mata daya zuwa sauran.”

A wani labarin, Wata mata ta yanke shawarar canza labarin aure ta wani siga da ba a san shi ba. Matar da ba a gano ko wacece ba ta auri maza 7 ita kadai.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Twitter na @blog_street, matar da dukkan mazajen nata suka kewayeta ta bayyana cewa tana kula da bukatunsu ita kadai kuma har ta gina wa kowannensu gida.

Matar ta ci gaba da bayyana cewa ragamar komai na a hannunta kan abun da ya shafi yin jima'i domin ita ke yanke shawarar da wanda za a yi a cikinsu.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


0 Response to "Burina shine in auri mata 20 - Mutumin da ya auri mata 12 ya haifar da cece-kuce a sabon bidiyo"

Post a Comment

Rubuta ra ayin ka

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN