Buhari ya sha alwashin daukan mataki kan 'yan bindiga, barazana ga rashin abinci


Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace mulkinsa zai yi amfani da duk wata dama da dabaru da ya sani wurin yin maganin 'yan bindiga domin tabbatar da samuwa abinci a damina mai zuwa.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, shugaban kasan ya sanar da hakan ne ga manema labarai na gidan gwamnati jim kadan bayan kammala sallar idi a ranar Alhamis.

Kamar yadda yace, matsalar 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane za a shawo kanta domin tabbatar da cewa kasar bata fada kalubalen rashin abinci ba.

Shugaban kasan wanda yayi fatan samun damina mai kyau, ya ce: "Hukumomin tsaro suna aiki wurin dawo da karfin guiwar jama'a, ta yadda zasu koma gonakinsu.

"Wannan na da matukar amfani. Wannan ne abinda hukumomin ke yi a yanzu. Muna so jama'a su koma gona ta yadda zamu samu abinci isasshe a kasar nan har mu samu na fitarwa waje."

A yayin bayanin kokarin ganin shawo kan matsalar tsaro a kasar nan da mulkinsa ke yi, Buhari ya janyo hankali kan tarukan da ya dinga yi a makonnin da suka wuce inda yace hakan yana daga cikin matsayarsu da shugabannin tsaro.

A wani labari na daban, shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulerasheed Bawa, yace dawo da tsohuwar ministan fetur, Diezani Alison Maduke gida tare da gurfanar da ita ba wasa bane.

Ya ce saboda tsohuwar ministar bata karkashin ikon Najeriya a yanzu tare da kalubalen da za a iya fuskanta wurin dawo da ita har yau sune manyan kalubale.

Wannan na kunshe a wata mujallar EFCC mai suna EFCC Alert wacce aka fitar a watan Afirilu, The Punch ta ruwaito.

Source: Legit Newspaper


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN