Babu Wani Makami da Zai Yi Nasara Kan Matsalar Tsaro Matuƙar Mutane Na Cikin Talauci, Sanatan APC


Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, yace matuƙar ba'a magance talauci da rashin adalci a Najeriya ba, to babu wani makami da zai yi nasara a yaƙin da ake da rashin tsaro a ƙasar nan.

Okorocha, wanda yayi jawabi a wajen taron shekara-shekara na 2021 NBA, mai taken "Rawar da mutane zasu iya takawa a gwamnatin Najeriya', yace akwai dangantaka tsakanin talauci da rashin adalci.

Sanatan ya kuma yi fatan Najeriya zata cigaba da kasance wa tsintsiya ɗaya duk kuwa da kiraye-kirayen a raba ƙasar da wasu keyi daga sassa daban-daban, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Okorocha yace:

"Bai kamata mu cigaba da tunanin cewa Najeriya zata tarwatse ba, Najeriya babbar ƙasa ce kuma ba zata tarwatse ba, bada jimawa ba za'a haifi sabuwar Najeriya."

"Akwai talauci da rashin adalci a cikin Najeriya, kuma waɗannan abubuwa biyu sun da dangantaka da juna."

"Matukar ba'a magance rashin adalci da talauci ba, to ko da zaku siyo dukkan makaman duniya domin yaƙar matsalar tsaro, bana ganin za'a samu sakamako mai kyau."

A wani labarin kuma Mutuwar COAS Ibrahim Attahiru Ya Ƙara Jefa Mu Cikin Matsaloli, inji Shugaba Buhari

Shugaba Buhari yace mutuwar shugaban rundunar Soji da sauran jami'ai 10 ya ƙaro matsaloli a ƙasar nan, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Shugaban yace Allah ne kaɗai yasan da faruwar wannan lamarin, amma ya faru a lokacin da ƙasar ke cikin ƙalubalen tsaro.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN