An damke hadimin gwamna Sule, yan sanda 2, Kansila da wasu 14 kan satan karafunan layin dogo


Hukumar yan sandan jihar Nasarawa ta damke mai baiwa gwamna Abdullahi Sule shawara kan ayyukan alfanu da wasu mutum 16 kan laifin sace karafunan layin dogon jirgin kasa.

An damke wadannan mutane ne suna satan karafunan dake garin Lafiya da karamar hukumar Keana na jihar.

Kwamishinan yan sanda CP Bola Longe, ya bayyana hakan ranar Alhamis a Lafiya, inda ya bayyana mutanen.

Ya yi bayanin cewa mutanen da ake tuhuman sun kasance suna kasuwancin sayan karafunan layin dogo daga wajen barayi amma dubunsu ya cika yayinda yan sanda suka samu labari.

"Hukumar yan sanda ta cika hannu da malalata yayinda suke satan karafunan layin dogo a Agyaragu dake karamar hukumar Lafiya da kuma Anguwan Alago dake karamar hukumar Keana," yace.

Yayinda Jaridar Punch taji ta bakin hadimin gwamnan, ya yi bayanin cewa bai san kayan sata ake sayar masa ba.

Yace: "Ni dan kasuwa ne. Ina da dillali mai kawo min kaya kuma na yadda da shi. Ya rasu yanzu.... Wannan shine karo na farko da suka kawo min karafunan layin dogo. Bayan da na saya, na sayar N3.6 million."

Daga cikin wadanda aka damke akwai jami'an yan sanda 2, jami'in NSCDC 1, tsohon Kansila 1 da kuma wani dan kasar Sin.

Source: Legit

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN