Wani soji da ke cikin sojin da ke yaki da Boko Haram a Borno mai suna Kila Jima ya kashe kanshi.
Sahara reporters ta ruwaito cewa sojin yana Bataliyan soji ta 152 da ke Banki, ya dana bindigarsa ya harbi kanshi da ita a kai ranar Asabar 10 ga watan Aprilu.
An ce alamun matsanancin damuwa ya bayyana tattare da sojin kafin ya kashe kanshi. An kai gawarshi Mutuwaren soji da ke Maiduguri domin adanawa.
Soji da dama da ke yaki da Boko Haram sun kashe kansu. A watan Maris, wani soji mai suna Bello Useni da aka dauko daga makarantar koyarwa na sojin surke da ke Bauchi ya kashe kanshi.
A watan Satumba 2020, wani soji Lance corporal da ke 27 Task Force Brigade a Buni Gari da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe ya kashe kanshi a wajen da yake aiki.
Haka zalika a 2019, wani soji ya rataye kanshi ya mutu a Abuja.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI