Ramadan: Bambanci tsakanin azumin Musulmi da na Kirista


Azumin watan Ramadan yana daya daga cikin ginshikan Musulunci guda biyar da suka wajaba a kan kowane Musulmin da ya kai munzalin yi - baligi, mai hankali, kuma mai cikakkiyar lafiya.

Kamar yadda yake a Musulunci, mabiyan wasu addinai ma kamar addinin Kirista suna gudanar da azumi.

Sai dai akwai bambance-bambance tsakanin azumin mabiya addinin Musulunci da kuma na Kirista - ko da yake dukkansu suna yin azumin domin neman kusanci ga Ubangiji.

Malamai da dama sun bayyana cewa bambance-banbancen sun hada da cewa Musulmai na yin azumi na kwanaki 29 ko kuma talatin kamar yadda hadisi ya tabbatar daga Manzon Allah (SAW) cewa, wata a Musulunci yana yin kwana 30 ne ko kuma 29, don haka azumi zai iya kasancewa kwana 30 ko 29.

Amma kuma bayanai sun nuna cewa a addinin Kirista ba haka ba ne wanda su azuminsu na kwana 40 ne domin sun yi imanin cewa annabi Isa (AS) ya zauna kwanaki 40 bai ci abinci ba wanda aka ruwaito cewa a wannan lokacin ya yi sadaka ya yi addu'oi yayin azumin.

Ustaz Murtala Muhammad Gusau, limamin Masallacin Jumma'a ne da ke garin Okenen jihar Kogi a Najeriya, kuma shugaban wata cibiyar yada addinin Musulunci da karantarwa a garin na Okene, kuma a tattanawarsu da BBC ya ce akwai banbance-banbance sosai tsakanin azumin Muslmai da na Kirista har ma da na Yahudanci.

''Azumi dai shi ne bautawa Allah ta hanyar kamewa daga cin abinci da abin sha da jima'i, tun daga hudowar alfijir har zuwa faduwar rana''.

A kowace shekara cikin watan Ramadan Musulmai a fadin duniya na gudanar da azumin kwanaki 29 ko 30, wanda ya sha banban da na mabiya addinin Kirista da na Yuhudanci da su kan yi azumin kwana 40 ne.

Ya kara da cewa ''Amma duka manufarsu kusan daya ne - Musulmai na yin azumi a bisa bin umarnin Allah da nufin gyara dabi'u da halayyar al'umma ta zama mai tsoron Allah, sannan kuma a tunatar da Musumai game da watan da aka saukar da Alkur'ani mai girma wato cikin watan Ramadan.''

Sheik Ibrahim Adamu Disina wani fitattaccen malami ne a jihar Bauchi arewa maso gabashin Najeriya, ya yi wa BBC karin bayanin cewa Musulmai kan fara azumi tun daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana inda su kan kauracewa ci da sha da jima'ai.

''Musulmai na azumtar kwanaki 29 ko 30, yayin da Kiristoci ke azumtar darare 40 da yini 40 ko kuma kwana 40, amma ko wanne akwai banbance-banbance ajen yanayin da bangarorin biyu ke azumin''.

''Kiristoci kan yi azumin ne ba tare da ya hana musu cin wasu abubuwa ba,'' in ji shi.

Haka shi ma Ustaz Murtala ya yi karin bayani cewa , Kiristoci na yin azumin a duk shekara amma kuma kamar yadda Musulunci ya tanadi cewa ya zama wajibi a kan duk Musulmi baligi, mai cikakkiyar lafiya ya dauki azumin watan Ramadan ba, su Kiristoci ba kowa ne ya ke yi ba kua bai zama wajibi ba.

''Yawanci malamansu da sauran jagororinsu ne kawai suke yin azumin, sannna kuma suna iya zamantowa mutum gashi yana azum amma zai iya cin wasu abubuwa abin sha ne kawai ba za i sah ba, ko kuma ya kasance ba zai ci ba gaba daya har tsawon kwana 40,'' in ji malamin.

Short presentational grey line

Yahudawa ma na azumi

Malam Murtala Muhammad ya bayyana cewa baya ga mabiya addinin Kirista, mabiya addinin Yahudanci ma na nasu azumin, kuma yana da kaman da na Kiristoci.

''Kamar yadda muke da azumi a addinan Musulunci da na Kirista haka su ma mabiya addidin Yahudanci ke yi, domin tunawa da Annabi Musa (AS) a lokacin da ya je ya karbo wa allunan nan masu ƙunshe da umarni goma daga Ubangiji a a kan tsaunin Sinai", ya ce.

''Duka dai don kauce wa aikata ayyuka marasa kyau - manufar ita ce a samar da al'umma masu tsoron Allah, masu imani, masu tausayi''. ''Masu addinin Yahudanci su ma kamar mabiya addinin Kirista ba kowa ne ke yin azumin ba , amma Musulmai duk kowa da malamai da masu arziki da talakawa ya wajaba a kan su.''

Azumi a addinin Kirista

A bangaren azumin mabiya addinin Kirista, Rabaren Joseph John Hayab shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Katsina, ya yi wa BBC karin bayani cewa Littafin Injila mai tsarki ya koya wa mabiya addinin Kirista su yi azumi.

Ya kuma ce Yesu Kiristi wanda shi ne tushen addinin na su shi ma ya yi azumi wanda ya nuna cewa idan akwai wasu matsaloli da suka addabi mutum ko kuma al'umma, hanyar magance su shi ne azumi da addu'a.

Malamin addinin Kirista din ya kuma ce zzumi wani babban abu ne a cikin addinin Kirsita, amma sai dai akwai banbaci tsakanin yadda mabiya addinin Kirsita ke yi da kuma na Musulmai.

''Bambancin da ke akwai na azumin da Kirsistoci ke yi da kuma sauran addinai shi ne mu muna azumi ne a kullum domin mu kara samun karfi wajen neman albarkar Allah a rayuwarmu.''

''Ba mu da waki kayyadajjen lokaci da aka ce za mu yi azumi kamar yadda a Musulunci ake yi da watan Ramadan,'' in ji Rabaren John.

Amma kuma Rabaren din ya yi karin bayanin cewa akwai wani lokaci da wasu bangarorin mabiya addinin Kirsita ke yin azumin kwana 40 da ake kira ''Lent'' wanda ba kamar na Ramadan ba shi ba doka ba ne sai wanda ya ga zai iya zai yi domin neman kusanci da Allah.

''A Kiristanci idan ka zabi za ka yi azumi ya danganta ga yadda ka tsara, ba ma yin kamar yadda musulami ke da kayyadaccen lokacin sahur ko kuma lokacin buda-baki, da ka gama cin abincin dare ka yi barci za ka tashi da azuminka ne, kuma za ka iya zaɓar lokacin da ka ga dama ka yi buda-baki,'' ya ce.

''Zan iya cewa akasarin Kirsitoci ba sa yin irin wannan azumin, amma kamar masu bin darikar Katolika da Angalika da sauransu, su kan lura da wannan lokaci na Lent su yi azumi,'' ya ce.

''Kuma suna yi ne domin biyayya da kuma bin gurbin Yesu wanda kafin ya fara hidimarsa ta bushara ya dauki kwanaki 40 yana azumi, wanda Kiristoci kan yi gabanin bukukuwan Easter,'' ya kara fada.

Azumin mabiya addinin Kirista din in ji Rabaran John ya babanta da na Musulmai ta hanyoyi da dama, musamman ma da yake ba kowa ne yake yin azumin ba a Kirstance, kuma wadanda ke yi suna daukar wa kan su iya lokuta da kuma kwanakin da suke son su yi azumin.

Galibi in ji malamin Kiristoci kan ƙuduri yin azumi idan suna da wata bukata da suke so Allah ya biya musu, kamar neman mijin aure, lafiya, gyara rayuwar iyali da 'ya'ya, da neman kariya ko kuma sauki daga abkuwar bala'o'i, da dai sauran bukatu na rayuwa.

Wani bambancin da Rabaran din ya bayyana wanda ke tsakanin azumin Musulmai da mabiya addinin Kirista ba sa bayyana cewa suna azumi kamar yadda Musulmai ke yi idan za su fara da kuma kammala azumin watan Ramadan ba.

''Littafin Bible ya koya mana cewa idan za mu yi ibada mu yi ta da a cikin zuciyarmu ba a bayyane ba don mutane su gani ba, amma duk da haka akwai Kiristoci da suka tallata azumi mukan fadakar da su cewa wanna wani abu ne tsakanin mai bi da kuma Allah da bai kamata mu bayyana ba.''

Muhimman abubuwa shida da suka banbanta azumin Muslmai da Kiristoci

Sheik Disina ya shaida ya yi wa BBC karin bayani cewa akwai wasu muhimman abubuwa shida da suka banbanta azumin Musulmai da kuma na Kirista, kuma ya jero su kamar haka:

  • Azumin Musulmai na amfani da lissafin watan sama ko shekarar kamariyya, yayin da Kirstoci ke lissafi da shekarar miladiyya ko shekarar shamsiyya.
  • Musulmai na azumtar azumin watan Ramadan ne a duk shekara, yayin da Kiristoci ke azumtar watan Afrilu da kwanaki 10 na watan Mayu a kowace shekara.
  • Musulmai na azumtar kawanaki 29 ne ko 30, amma kiristoci suna azumtar darare 40 ne da yini 40 ko kuma kwanaki 40.
  • A Musulunci azumi dole ne ga baligi lafiyayye mazaunin gida, sannan ƙin yin azumi ga wanda ya wajaba a kansa yana iya warware Musuluncin mutum, amma a addinin Kirista yin azumi alama ce kawai ta nagartar bawa da cikakkiyar biyayyarsa ga Yesu Almasihu amma rashin yin azumi ba zai iya cire shi daga Kiristanci ko kuma a ce ya yi wani babban laifi ba.
  • .Azumi a wurin Musulmai yana farawa ne daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana - mutum zai kame daga ci da sha tun daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana, yayin da su kuma Kiristoci azuminsu yana farawa ne daga cikin dare, daga zarar mutum ya yi barci sai kuma in Allah ya kai mu washegari in rana ta fadi.
  • A addinin kirstanci an bayyana cewa ana so bawa ya boye azuminsa hatta wa iyalansa, yayin da a Musulunci kuma azumi ibada ce ta gangami da jagoran musulmai ke sanar da fara shi da kuma kare shi.
  • Rahotun BBC Hausa

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN