Pantami ya cire takunkumin rijistan layin waya, yace a cigaba da yin rijistan


Gwamnatin tarayya ta bada izinin cigaba da rijistan sabbin layukan waya bayan wata da watanni da sanya takunkunmin yin haka.

Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami, ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa, Dr Femi Adeluyi, ranar Alhamis a shafin Tuwita.

Ministan ya ce za'a cigaba da rijistan amma da sharadin sai mutum na da lamban katin zama dan kasa, NIN.

Pantami ya ce an yanke shawaran cigaba da rijistan sabbin layuka ne bayan amincewar shugaba Buhari da sabon tsarin rijistan layuka da ma'aikatarsa ta samar.

"An kammala gyara-gyare kan tsarin bisa ga umurnin shugaban kasa inda aka wajabta amfanin da lambar NIN don rijisttan sabon layi a jiya, 14 ga Afrilu, 2021," jawabin yace.

"Dr Pantami ya gabatar da tsarin ga shugaba Muhammadu Buhari...kuma (Buhari) ya jinjinawa ministan bisa kokarinsa wajen kawo cigaba sashen tattalin arzikin zamani da kuma atisayen hada layukan waya da NIN."

"Za'a fara aiwatar da sabon tsarin ranar Litnin, 19 ga Afrilu 2021. Hakazalika za'a cigaba da bada sabbin layuka da kuma sauran abubuwan da aka dakatar a ranar.

"Bugu da kari, Ministan ya umurci NCC da NIMC su tabbatar da cewa maus rijistan layukan da jama'a sun bi tsarin sau da kafa."

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN