Kebbi: Jirgin saman yaki NAF ya yi wa yan bindiga luguden bama bamai a Masarautar Zuru


Jirgin saman yaki na sojin sama na Najeriya ya saki bamabamai kan wasu Yan bindiga da suka farmaki kauyukan Kondunku da Bajida da ke rikon garin Kanya a karamar hukumar Danko-Wasagu ranar Talata 20 ga watan Aprilu.

Shafin ISYAKU.COM ya samo cewa Yan bindigan sun farmaki kauyukan ne da misalin karfe daya na rana, kuma suka yi ta tattara shanayen bayin Allah suna kora su.

Majiyarmu ta ce maharan sun so su farmaki kauyen Kangon Wasagu da farko, amma suka zarce suka bi ta kauyukan Binoni, Unashi Wasagu, har suka isa kauyukan Kondunku, Bajida da sauran kauyuka da ke rikon garin Kanya inda suka farmaki jama'a.

Majiyar ta ce an dakatar da Yan sa Kai da yansandan kwantar da tarzoma mopol daga shiga kauyukan da misalin karfe daya na rana. Daga bisani jirgin yaki na sojin sama ya iso ya yi wa Yan bindigan luguden bama bamai, irinsa na farko a tarihin yaki da Yan bindiga a Masarautar Zuru da ke kudancin jihar Kebbi.

Kimanin mutune 600 ne suka sami mafaka a garin Kanya bayan sun tsere lokacin da Yan bindigan suka shiga kauyukansu. Mutanen sun isa garin Kanya ne a cikin motoci kirar Toyota Canter da yawa.

Sai dai bayan da kura ta lafa da misalin karfe 5:30 na yamma ranar Talata, an gan dandazon jama'a suna komawa kauyukansu bayan Yan bindigan sun wuce.

An yi hasashen cewa shanu da yawan gaske ne Yan bindigan suka tattara suka kora.

Sai dai an ga wasu matan Fulani guda biyu da ake zargin Yan bindigan ne suka harbi daya a kafa, daya kuma suka harbe ta da bindiga a ciki. Lamari da ya sa ta cikin mumunan yanayi. An garzaya da matan zuwa Asibit domin samun kulawan Likita.

Kawo yanzu, Mahukunta a jihar Kebbi tare da hadin gwiwa da yansandan mopol, Yan sa Kai da sauran jama'a suna tattara bayanai kan lamarin da ya faru sakamakon farmakin Yan bindigan.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN