Duba abin da ya faru yayin da Gwamnan Kano Ganduje ya hau babur ɗin KAROTA da babbar riga


Bayyanar Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano a kan babur sanye cikin 'babbar riga' ya haddasa cece-kuce a shafukan sada zumunta.

Legit.ng ta rahoto cewa gwamnan ya tunawa yan Najeriya da zamanin tsohon gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti.

Fayose, a lokacin da yake mulki, an san shi da wasannin kwaikwayo daban daban wanda ke haifar da martani a shafukan sada zumunta.

Sai dai hawan babur din Gwamna Ganduje yana da wata manufa ta daban, ba kamar ta Fayose ba.

Ya hau kan daya daga cikin baburan ne lokacin da yake kaddamar da mashinan da hukumar KAROTA ta sayo don kula da zirga-zirga.

Yayin kaddamar da su a ranar Lahadi, 18 ga Afrilu, Ganduje ya ce za a yi amfani da su ne don tabbatar da cewa masu amfani da tituna sun bi ka’idojin zirga-zirga.

Ya ce baburan za su bai wa ma’aikatan KAROTA damar motsawa cikin sauri don lura da zirga-zirga, gano masu karya doka da kuma zagaye cikin gari don kamo wadanda ke shigo da haramtattun kayayyaki zuwa jihar.

A wani labarin, yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talat ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN