Yan bindiga sun farmaki kauyukan Sakaba, sun kashe DPO, yansanda 3 da Yan sa kai


Yan daban daji sun farmaki kauyukan karamar hukumar Sakaba da safiyar Lahadi 25/4/2021, sun kora kimanin shanaye 1000, tare da tafka mumunan ta'asa a yankin.

Shafin labarai na ISYAKU.COM ya samo cewa yan daban dajin, sun shiga yankin garin Makuku ne da kewaye tun karfe 9 na safe, suka yi ta tattara shanayen bayin Allah suna kora su.

Majiyarmu ta ce ana zargi, tare da fargaban cewa Yan daban dajin sun halaka babban jami'in yansanda DPO na karamar hukumar Sakaba,  yansanda 3 da wasu yan sa kai. 

Mun samo cewa jami'an tsaron sun fuskanci yan daban dajin ne bayan samun labarin farmakinsu, amma sai yan daban dajin suka yi masu kwanton bauna suka afka masu, lamari da ya haifar da mumunan zubar da jini tsakanin yan daban da jami'an tsaro da ke samun marawar baya daga Yan sa Kai.

Kawo yanzu dai, babu wani tabbaci kan adadin mutane da suka mutu a wannan artabu tsakanin jami'an tsaro da Yan daban daji wanda har karfe 9:30 na dare ana fafatawa tun karfe 9 na safe da Yan daban dajin suka shiga yankin.

Mun samo cewa, ana zargin jirgin saman yaki na sojin sama NAF, ya kai dauki domin marawa jami'an tsaro baya, amma Yan daban dajin suka boye a karkashin itatuwan Mangwaro da sauran itatuw. Daga bisani suka fito suka ci gaba da tafka ta'asa.

Kawo yanzu, babu alkalumma a hukumance na adadin wadanda suka rasa rayukansu a harin Yan daban dajin na ranar Lahadi. Sai dai ana kyautata zaton samun cikakken bayani daga mahukunta a jihar Kebbi ranar Litinin.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN