Da duminsa: Yan bindiga sun kashe soji 3, mopol 4 da fararen hula 7 a Danko-Wasagu


Ana zargin cewa soji 3 da yansandan kwantar da tarzoma 4 ne suka kwanta dama lokacin kare wani mumunan kwantan bauna da Yan bindiga suka yi masu a daren Laraba 7 ga watan Aprilu, a cikin dajin Wasagu da ke karamar hukumar Danko-Wasagu a kudancin jihar Kebbi.

Jami'an tsaron suna kan hanyarsu ce ta zuwa kare dukiyan al'umma bayan samun rahotun cewa yanbindiga sun kora shanayen bayin Allah.

Sai dai yayin da jami'an tsaron ke kan hanyarsu ta zuwa wajen, sai suka sami kansu a wani mumunan kwantan bauna da Yan bindigan suka yi a wani tsauni da ke cikin daji tsakanin kauyukan Kanwa, Minoni da Dadin kowa.

An yi zargin cewa Yan bindigan sun kasa kansu zuwa gida hudu, kuma suka rutsa da sojin bayan sun yi masu kawanya, a cewar majiya mai tushe.

Kuma nan take Yan bindigan suka bude wa jami'an tsaron wuta, sakamakon haka jami'an tsaro suka mayar da martani mai karfi, yanayi da ya rikide zuwa mumunan bata kashi tsakanin yan bindiga da jami'an tsaro.

Bayan da kura ta lafa, an lissafta asarar rayuka 3 daga bangaren soji, 4 daga yansandan kwantar da tarzoma, fararen hula guda 7 ciki har da Haliru Buzu wani Gwarzon Dan kare yankin Danko-Wasagu daga farmakin Yan bindiga, wanda ake zargin an shake shi ne har ya mutu domin babu raunin makami ko harsashi a jikinsa, sai dai alamun shakewa a wuyarsa kamar yadda majiya mai tushe ta shaida mana.

Wata majiya ta ce Yan bindigan sun kasa kora shanayen da suka koro sakamakon barin wuta da suka fuskanta daga jami'an tsaro.

Mai magana da yawun hukumar yansanda jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar, ya tabbatar da mutuwar yansanda masu mukamin Safeto guda 3 da mai mukamin Sajen guda 1 a gumurzu da aka yi. Sai dai bai yi bayani kan soji ko farar hula da aka kashe ba domin yansanda na kan tantance bayanai kafin fitar da rahotu kan lamarin.

Mun samo cewa mahukunta a karamar hukumar sun zagaya gidajen fararen hula da suka rasa rayukansu kuma suka yi masu jajen rashi da yin abin da ya kamata a matakin farko kan lamarin.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN