Da dumi-dumi: Ana Ci Gaba da Artabu Tsakanin Sojoji da Boko Haram a Geidam


Ana ci gaba da luguden wuta tsakanin sojojin Najeriya da masu tayar da kayar baya na kungiyar ISWAP a Geidam, jihar Yobe, Arewa maso gabashin Najeriya.

'Yan ta'addan sun dawo garin Geidam ne 'yan sa'o'i bayan da suka janye bayan da aka shafe sama da awanni 24 suna yi wa garin kawanya, farawa daga ranar Juma'a, 23 ga Afrilu.

An samu labarin a safiyar Lahadi cewa sojojin Najeriya da masu tayar da kayar baya a halin yanzu suna artabu sosai sakamakon wani sabon hari.

Wasu Mazauna Geidam tuni suka tsere sakamakon rikicin. Akwai fargabar cewa adadin masu tayar da kayar baya a cikin rundunar ya karu.

Ko da yake Sojojin Najeriya a ranar Asabar, 24 ga Afrilu sun ce, sun yi mummunan rauni a kan mayakan ISWAP a yayin artabun na baya, wani dan majalisar tarayya da ke musanta ikirarin.

Premium Times ta ruwaito cewa Lawan Shettima, dan majalisa mai wakiltar mazabar Geidam, Yunusari da Bursari a Majalisar Tarayya, ya ce har yanzu maharan suna da iko da garin Geidam.

“Zan iya gaya muku cewa wadannan maharan sun mamaye Geidam. Kuna iya ganin bidiyo da hotuna yayin da suke motsawa suke ta kona abin da suka ga dama,” in ji Shettima.

Dan majalisar ya kuma ce 'yan mazabarsa “sun kasance a karkashin rahamar kungiyar Boko Haram sama da awanni 24 ba tare da wani kalubale ba."

A wani labarin, Rundunar sojojin Nigeria ta ce dakarunta na Operation Lafiya Dole, a ranar Juma'a, ta ce dakarunta sun kashe ƴan ta'addan kungiyar Boko Haram/ISWAP a garin Geidam a Yobe.

Hakan na zuwa ne bayan rahotonni da ke nuna cewa ƴan ta'addan sun sake kai hari Geidam a ranar Juma'a kmar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin rundunar sojojin, Mohammed Yerima, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar ya ce sojojin sun kwato motocci masu bindiga da wasu makaman yayin artabu da yan ta'addan.

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN