Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura ya gudana a kasar Masar

Ranar Asabar 3 ga watan Afrilu ne kasar Masar ta gudanar da wani gagarumin bikin sauyawa tsoffin Fir'aunonin kasar kaburbura zuwa wani katafaren gidan adana kayan tarihi.

An yi jerin gwanon Fir'aunonin cikin kasaita, yayin dubban dubatan mutanen kasar suka yi dafifi a yayin bikin.

An makudan miliyoyin daloli domin bikin na nuna girmamawa ga kaburburan masu dunbun tarihin da ya haura shekaru sama da 3,000, in ji Rahoton Aljazeera.

Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana

Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana Hoto: aljazeera.com

An sauyawa Fir'aunonin 22 wajen zama, wadanda suka kasance 18 daga cikinsu wasu shahararrun sarakunane da kuma sarauniyoyi hudu.

Hukumomin kasar ta Masar ta rufe manyan hanyoyin da suka dangana da kogin Nilu domin nuna girmamawa ga a Fir'aunonin.

A tarihance, kasar na matukar alfahari da ajiyar sauran gawarwakin Fir'aunonin na tsawon tarihi.

Ga wasu daga cikin hotunan yadda bikin ya gudana a jiya Asabar.

Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana

Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana Hoto: aljazeera.com

Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana

Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana Hoto: aljazeera.com

Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana

Bidiyo da hotunan yadda bikin sauyawa Fir'aunoni kaburbura a kasar Masar a gudana Hoto: aljazeera.com

A wani labarin, Ana jerin gwanon fito da gawarwakin tsofaffin shugabannin Masar 22 da suka shude a Alkahira a yau Asabar inda za a sauya su zuwa wani sabon gidan adana kayan tarihi da ke kudancin birnin, BBC Hausa ta ruwaito.

Ana sa ran cincirindon jama'a za su yi jerin gwano kan tituna domin kallo - inda za su ga sarakuna 18 da sarakuna mata huɗu na Masar da za a dauka cikin akwatunan zinari.

Za a tsaurara matakan tsaro sosai, musamman daukarsu da ake a matsayin masu daraja kuma matsayin dukiyar kasar.

Source: Legit.ng

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN