Ƴan tawayen Chadi sun yi tayin sasantawa


Yan tawaye a arewacin Chadi da sojojin ƙasar suka zarga da kashe shugaba Idris Deby sun ce a shirye su tsagaita wuta da kuma tattauna batun sasantawa a siyasance, a cewar kakakin ƴan tawayen a ranar Lahadi.

Ƴan tawayen FACT a Chadi da ke arewacin Chadi kan iyaka da Libya a ranar 11 ga Afrilu suka tunkari N'Djamena, suna kiran kawo ƙarshen mulkin Idriss Deby na shekaru 30.

Sun kusan shiga N'Djamena, kusan tazarar kilomita 200 zuwa 300 kafin sojoji suka kore su.

An kashe Idriss Deby a ranar Litinin yayin da ya kai wa sojojin Chadi ziyara a fagen daga.


Mutuwarsa ta girgiza ƙasashen Tsakiyar Afrika da yankin Tafkin Chadi da Sahel saboda rawar da yake takawa ga yaƙi da ƴan bindiga.

Kakakin FACT Kingabe Ogouzeimi de Tapol ya shaida wa Kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa a shirye suke su tsagaita buɗa wuta da kuma tattaunar da ta mutunta ƴancin Chadi ba juyin mulki ba.

Bayan mutuwar Deby, Sojojin Chadi suka kwaci mulki inda suka ɗora ɗansa Mahamat Idriss

Deby tare da alƙawalin zai yi riƙon ƙwarya na watanni 18 kafin gudanar da zaɓe. Matakin da ƴan adawa da ƴan tawaye suka kira juyin mulki

Rahotun BBC Hausa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/IM8Uuxtia6qBsdKcEszx7s

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN