Yansandan Kebbi sun kubutar da yar shekara 2 da aka sace a Ambursa, sun kama mutum 3


Rundunar yansandan jihar Kebbi ta ceto wata yarinya mai suna Shafa'u Hussaini yar shekara 2 da haihuwa bayan an sace ta a garin Ambursa ranar 19 ga watan Maris.

Kakakin yansandan jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar ya shaida wa manema labarai haka a wata takarda da ya sa wa hannu amadadin Kwamishinan yansandan jihar Kebbi.

Takardar ta ce " Ranar 20/ 3/2021 da karfe 10 na dare wani mutum mai suna Hussàini Muhammed daga garin Ambursa a karamar hukumar Birnin kebbi ya kawo kara cewa diyarshi yar shekara 2 mai suna Shafa'u Hussaini ta bace da misàlin karfe 12 na rana, ranar 19 ga watan Maris.

Ya ce daga bisani wani ya kira shi ya ce shi kidnapa ne kuma dole ya ba su N500,000 idan ba haka ba za su kashe yarinyar.


Sakamakon haka yansanda masu bincike suka dukufa wajen aiki kuma suka ceto yarinyar. Bincike kuma ya kaimu ga kama wani mai suna Abbas Abubakar dan shekara 22 wanda makwabcin mahaifin yarinyar ne, 

A ci gaba da bincike Abbas ya tabbatar wa yansanda cewa ya hada baki ne da wata mai suna Hadiza Ahmed mai shekara 30, wacce itama makwabciyar mahaifin yarinyar ne, amma aka hada kai da ita aka sace Shafa'u suka kai ta wajen wata mata mai suna Zainab Ahmed mai shekara 35 a garin Gulumbe.

Yansanda sun mayar da Shafa'u wajen iyayenta, yayin da ake shirin gurfanar da wadanda ake zargi a gaban Kotu". Inji DSP Nafi'u Abubakar.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE