Yan sanda Sun cafke Mambobin IPOB 16 da bindigu da Bama-Bamai


Rundunar 'yan sandan Najeriya ta cafke mambobin ƙunguyar dake ikirarin kafa ƙasar biyafara IPOB 16 da kuma kwato bindigu da bama-bamai a hannunsu. Jaridar legit ta ruwaito.

Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da mai magana da yawun rundunar, Frank Mba, ya fitar a ranar Lahadi 28 ga watan Maris, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Hukumar yan sandan ta zargi waɗan da aka kama ɗin da haɗa baki wajen tada rikice-rikice da kuma kai hari ga jami'an tsaro da kayayyakinsu a yankin kudu maso gabashin Najeriya da ma wasu sassan ƙasar nan.

Legit.ng ta gano cewa an sami wannan nasarar ne bayan aikin haɗin guiwa tsakanin yan sanda, sojojin ƙasa, da sojojin sama domin kamo mutanen da ke da alhakin kai ma jami'an tsaro hari da kuma bata wurare da kayayyakin jami'an.

Waɗan da aka kama sun haɗa da; Ugochukwu Samuel, ɗan shekara 28 daga karamar hukumar Arochukwu Jihar Abia; Raphael Idang, ɗan shekara 31 ɗan karamar hukumar Odukpani jihar Cross River.

Sauran sun haɗa da Cletus Nwachukwu Egole, ɗan kimanin shekara 60, ɗan garin Orlu jihar Imo; da kuma Michael Uba, shima ɗan jihar ta Imo.

Sai dai ba'a bayyana sauran mutum 12 ba.

'Yan sandan sun bayyana cewa, binciken da suka gunar ya nuna mutanen na da hannu a mafi yawancin tashin hankullan da aka yi a yankin kudu maso gabashin ƙasar nan.

"An kama waɗan da ake zargin a sassa daban-daban na ƙasar nan bayan juriya, da kuma saka fasaha a aikin." A cewar mai magana da yawun yan sandan.

Hukumar ta kuma ƙara da cewa, dukkan su za'a gurfanar da su a gaban kotu bayan an kammala bincike.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN