Uwar yara 2 ta mutu yayin da saurayi ke tsakiyar aikata lalata da ita, duba silan lamarin


Wata mata mai shekaru 37 wacce ked a haihuwar ‘ya’ya biyu ta mutu yayin holewa da masoyinta a Yola, babban birnin jihar Adamawa. Jaridar legit hausa ta ruwaito.

Yan sanda sun kama masoyin nata mai suna Lekan Agboola, wanda ya kasance injiniya a kamfanin sadarwa.

DSP Suleiman Nguroje, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Adamawa, ya ce Agboola, wanda a yanzu haka yake tsare a sashin binciken manyan laifuka na rundunar, yana da mata da yara biyu, suna zaune a Legas.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Agboola ya furta cewa marigayiyar ya kasance budurwarsa fiye da shekaru uku.

Da yake bayanin abin da ya faru a ranar da ta mutu, Agboola ya ce, “A ranar 24 ga Fabrairu, 2021, da misalin karfe 9 na safe, na kira ta a waya na ce ta zo ta gan ni saboda ba mu ga juna ba na wani lokaci. Lokacin da ta iso, mun fara holewa sai kwatsam ta faÉ—i.

“Lokacin da na fahimci ba ta numfashi, sai na kira daya daga cikin abokaina mata na fada mata abin da ya faru. Ta shawarce ni da in kai ta asibiti inda aka tabbatar da cewa ta mutu.”

Nguroje ya ce ‘yan sanda na kokarin binciken ainihin abin da ya sa matar ta mutu.

A wani labarin, tsohuwar matar tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigon jam'iyyar PDP, Femi Fani-Kayode, Precious Chikwendu ta maka tsohon mijinta a gaban kotu da bukatar karbar 'ya'yan da suka haifa.

Precious ta maka Fani-Kayode a gaban wata babban kotun tarayya dake Abuja inda take bukatar karbar 'ya'yanta hudu da suka haifa yayin da suke tare, amma a bar mahaifinsu ya dinga zuwa ganinsu, The Nation ta wallafa.

Matar mai son Fani-Kayode da duk wasu mukarrabansa su kiyayi kwace mata 'ya'yanta ta karfi da yaji, ta bukaci kotun da ta sa tsohon ministan ya dinga biyanta N3.438 miliyan duk wata domin kula da yaran tare da wasu kudi na daban domin karatunsu da sauran bukatunsu.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN