Tap di Jan: Basarake ya kwada wa tsohon Gwamna sanda a cikin jirgin sama, duba dalili


Tsohon shugaban Majalisar Sarakunan gargajiya na jihar Imo Eze Cletus Ilomuanya ya kai wa tsohon Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha hari a cikin jirgin sama ranar Lahadi 28 ga watan Maris.

Basaraken ya fuskanci tsohon Gwamnan ne a cikin jirgi a lamari da ya fara kamar wasa amma ya rikide zuwa babban lamari a sashen daukan kaya na filin jiragen sama na kasa da kasa na Sam Mbakwe da ke birnin Owerri a jihar Imo, inda basaraken ya kwada wa tsohon Gwamnan jihar Imo sanda da yake riike yana tafiya da ita a cikin jirgin sama kuma ya yi ihu yana cewa " Ka rabu da al'amarin mutanen Orlu!".

 

An dakatar da rigimar ne bayan Kaptin na jirgin tare da sauran ma'aikatan jirgin sun shiga tsakani, tsohon Gwamnan jihar Imo Okorocha bai rama dukan da sanda da basaraken ya yi masa ba , kuma ya  nuna juriya da hakuri, domin daga karshe ya canja wajen zama ya bar wa basaraken wuri wanda ya ci gaba da tsangwaman tsohon Gwamnan ta hanyar ci gaba da babatu.


Mun samo cewa Ilomianya yana daya daga cikin Sarakunan gargajiya da tsohon Gwamna Rochas Okorocha ya tsige a watan Yuni  2014 bayan an tumbuke shi daga mukamin shugaban Majalisar Sarakunan gargajiya na jihar Imo, amma Gwamna Emeka Ihedioha ya mayar da shi bisa shawarar masana shari'a.


Sai dai tsohon Gwamnan ya fitar da jawabi kan lamarin ta hannun mai ba shi shawara kan harkar labarai Sam Onwuemeodo, inda ya ce harin basaraken kan tsohon Gwamnan abin kunya ne da bai dace da kimarsa ba.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN