Tambuwal ya gwada mota kirar Najeriya mai aiki da wutan lantarki


Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya amshi motar Kona mai aiki da Wutar Lantarki wacce Hukumar Kula da kera motoci da cigaban motoci ta kasa (NADDC) tare da hadin gwiwar kamfanin Stallion suka bude kwanan nan. Jaridar legit ta ruwaito.

Ku tuna cewa a ranar 5 ga watan Fabrairu, NADDC, a karkashin jagorancin Darakta-Janar na ta, Jelani Aliyu, ta gabatar da motar mai aiki da lantarki ta farko da aka kera a cikin gida mai suna Hyundai Kona, a Abuja.

Motar an sanya mata farashin Naira miliyan 24 ga kowane daya, tare da ba da garantin batir da kira na tsawon na shekara 5, 100% aiki da lantarki, ba amfani da mai za kuma a iya cajinta a gida da wajen aiki, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da yake jawabi bayan gwajin motar a gidan gwamnati na Sakkwato, Gwamna Tambuwal ya yaba da shirin, yana mai bayyana shi a matsayin wani sauyi na al'adu wanda zai shafi rayuwa da kuma damar 'yan Najeriya matuka.

A cewar Tambuwal, yana da kyau cewa yayin da nasarorin kimiyya a duniya ke turawa zuwa daina amfani da mai, Najeriya tana da nasarori irin na fasaha kamar mota mai aiki da lantarki da za ta kawo sauyi kan yadda ake ginin gidaje da kiyaye su, gina hanyoyi, da kuma sarrafa su.

Don haka gwamnan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakan da suka dace wajen amfani da damar da Jihar Sakkwato ke da shi don tallafawa wajen fadada tattalin arzikin jihar.

Tambuwal, wanda ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da yake tuka mota mai amfani da lantarki, ya bayyana fasahar a matsayin mai ban sha’awa da kuma kyakkyawar muhalli, ya kara da cewa fasahar ta fi rahusa ta fuskar kulawa.

Gwamnan, yayin bayyana Mista Aliyu a matsayin babban jakadan jihar, ya ba da tabbacin goyon bayan sa ga NADDC a kokarinta na sauya fasalin kamfanin kera motoci na kasar.

Ya kuma yabawa babban daraktan NADDC bisa halartar kasuwar baje kolin, yana mai cewa kasancewarsa ya jawo zuba hannun jari da dama a jihar da yankin.

An gabatar da motar a wani baje kolin Kasuwanci na jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara da ke gudana a Sakkwato, shugaban NADDC din dan shekara 55 ne ya gabatar da ita.

Shugaban na NADDC ya kasance tsohon ma'aikaci a America's General Motors wanda ake alfahari dashi don zanen wata mota a 2004 Pontiac G6 da 2010 Chevrolet Volt.

A wani labarin, Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP a 2019 Atiku Abubakar, ya shawarci gwamnatin Buhari kan hanyoyin da za ta bi ta magance matsalar rashin aikin yi a Najeriya.

Atiku ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wani rahoto da Bloomberg ta fitar cewa Najeriya, itace kasa mafi yawan mutanen da ke fama da talauci a duniya, da alama kuma za ta sake karya wani tarihin na zama kasa mai mafi yawan marasa aikin yi a duniya.

Atiku, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter kuma jaridar Legit ta gano ya bayyana cewa, gwamnatin mai ci a Najeriya na bukatar taimako don ceto kasar baki daya.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN