Ta faru ta kare: Matawalle ya tona asirin wanda ke daure wa yan bindiga gindi a Zamfara


Bello Mohammed Matawalle, gwamnan jihar Zamfara, ya bayyana cewa wasu yan siyasa da giyar mulki ke diba a jihar wadanda ke zama a Abuja sune silar sace-sacen mutanen da addabi jihar. Jaridar legit ta ruwaito.

PM News ta ruwaito cewa gwamnan ya sha alwashin kama duk wani dan siyasa da ya shiga jihar tare da kudirin amfani da bata gari wajen haddasa fitina.

Legit.ng ta tattaro cewa ya ce babu wani da zai yi ikirarin fin karfin doka a kasar, cewa ya saka kafar wando daya da makiyan zaman lafiya a jihar.

Ya bayyana hakan a gidan gwamnati da ke Gusau, babbar birnin jihar, lokacin da tawagar kungiyar gwamnonin Najeriya karkashin jagorancin Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti suka kai masa ziyara kan sakin daliban makarantar Jangebe a ranar Talata, 2 ga watan Maris.

Matawalle ya yi gargadin cewa babu wanda ya tsarkaka ko ya fi karfin a taba shi, inda ya bayyana cewa shine ke da ragamar kula da harkokin jihar Zamfara, inda ya kalubanci duk wani dan siyasa da ya kiyaye shi ko ya ga aiki da cikawa.

Gwamnan ya bayyana a ranar Lahadi, 28 ga watan Fabrairu, lokacin da tawagar gwamnatin tarayya ta ziyarce shi cewa mutane da dama za su sha mamaki idan ya fallasa wadanda ke daukar nauyin yan bindiga.

Ya bayyana cewa manyan mutane da dama na da hannu a ta’addanci a jihar sannan cewa ba da jimawa ba zunubinsu zai fallasa su.

A wani labarin, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya mayar da martani ga shawarar da Majalisar Tsaro ta Kasa ta yanke na ayyana jihar ta Zamfara a matsayin haramtaccen yanki ga jirage, Daily Trust ta ruwaito.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya), ne ya bayyana hakan a karshen taron majalisar tsaron kasa da aka yi ranar Talata.

Monguno ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta hana ayyukan hakar ma’adanai a jihar.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN