Ta banka wa al'aurar yar shekara 8 wuta da ashana bayan duka da wayan wuta, duba dalili


Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta kama wata matar aure mai suna Aisha Abdullahi Gaide, bisa zargin yi wa diyar kishiyarta dukan cin zarafi da yunkurin aikata kisan kai.

Kakakin yansandan jihar Bauchi SP Ahmed Mohammed Wakil, ya shaida wa manema labarai a wata takarda da ya fitar cewa, ranar Litinin 1 ga watan Maris, Aisha ta yi wa Zahra Abdullahi duka da wayar wuta, kuma ta kyasta ashana tana ci da wuta ta saka wa Zahra a al'aurarta, lamari da ya sa ta sami tsananin kuna a wajen.

Zahra diyar kishiyar Aisha ce kamar yadda wata majiya ta labarta, sai dai kishiyar bata gidan a halin yanzu. 

Kazalika Kakakin yansandan ya ce Aisha ta yi wa Zahra wannan duka da azaba ne kawai domin ta yi tuntube da ita lokacin da take kwance.

Aisha na hannun yansanda sashen CIID tana ci gaba da amsa tambayoyi.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN