A kalla shanu 50 ne suka mutu a wani yanayi mai daure kai a Akungba-Akoko, a karamar hukumar Akoko na jihar Ondo, Vanguard ta ruwaito.
Kazalika Jarida legit ta ruwaito cewa an gano cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da yamma a yankin Ibaka na garin.
Wani mazaunin Akungba, Oshk Fela Castro ya shaidawa SaharaReporters cewa shanun sun mutu ne bayan cin wani abu da ake zargin guba ne.
Ya shawarci mazauna garin su guji sayar nama mai araha domin yana zargin wasu masu sayar da nama marasa gaskiya za su iya sayar da naman shanun da suka mutu.
"Bayanin da na samu shine shanun sun mutu bayan cin wani abu da ake zargin guba ne. Kuma an fada min cewa duk wanda ya ci naman zai iya mutuwa saboda gubar. Shanun sun fara rubewa bayan minti 30 bayan mai su ya gano sun ci guba.
"Don Allah ku fadawa makwabta da abokanku su yi takatsantsan wurin siyan nama. Ina son jami'an tsaro su tabbatar ba a siyar da naman wadannan shanun da suka mutu ba," in ji shi.
A 2019, an ruwaito cewa tsawa ta kashe kimanin shanu 36 a Ijare, karamar hukumar Ifedore a jihar Ondo.
Duk da ikirarin da wasu mazauna garin suka yi na cewa tsafi ne ya kashe shanun saboda Fulani sun keta cikin wurin bautar masu addinin gargajiya, yan sanda sun ce tsawa ce kawai.
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI