Rundunar sojin MNJTF za su iya kawo karshen Boko Haram, inji Idris Deby


Jaridar legit ta ruwaito cewa shugaban Æ™asar Chadi, Marshal Idris Deby Itno, ya bayar da tabaccin cewa rundunar sojin haÉ—aka zasu iya kawo Æ™arshen ta'addancin Boko Haram, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ƙasar Chadin a ranar Asabar ya tabbatar da hakan yayin amsa tambayoyin manema labaran cikin gidan gwamnati a fadar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bayan ziyarar kwana daya da ya kawo.

Shugaban Chadin ya cigaba da bayyana yadda ta'addanci yake cigaba da ciwa kowa tuwo a ƙwarya musamman a yankin tafkin Chadi da yankin Sahel a Afirika saboda MNJTF basu fara aiki a wuraren ba.

A cewarsa, ya tattauna da Shugaba Buhari akan MNJTF inda yace da zarar sojojin haÉ—in guiwar sun fara ayyukansu na tsawon shekara É—aya zasu ci galaba akan ta'addanci.

Itno ya bayar da yaƙininsa har yake ƙara bayyana cewa jam'an sun zo da sababbin dabaru na musamman ta yadda cikin sauƙi zasu cimma gaci tun daga yankuna zuwa iyakokin ƙasashe don kawo ƙarshen 'yan Boko haram da mayaƙan ISWAP har abada.

A cewarsa sun tattauna akan wasu matsalolin da suke addabar Najeriya da ƙasar Chadi a taron da sukayi.

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da rashin fahimtar hoton da Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya gabatar masa a fadar shugaban kasan dake Abuja.

Tun a farkon makon nan, Buhari ya karba bakuncin Ganduje wanda ya nuna masa hoton gadar Muhammadu Buhari da za a yi a jihar Kano.

A yayin zantawa da BBC Hausa, Kwankwaso yayi mamakin dalilin da zai sa a karba bashin N20 biliyan a kan aikin nan, wanda yace aikin gwamnatin tarayya ne.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN