Kwankwaso ga Ganduje: Ilimi diyan talakawan Kano ke bukata fiye da gada


Tsohon Gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya soki shirin gina gadan sama na ababen hawa da Gwamna Ganduje ke shirin yi a shataletalen Hotoro da ke birnin Kano da kudin bashi.

Kwankwaso ya caccaki Gamduje sakamakon karbo bashin Naira biliyan 20 domin gina gadan. Ya ce Gina gadar aikin Gwamnatin Tarayya ne ba na Gwamnatin jihar Kano ba.

A cikin wannan mako ne Gwamna Ganduje ya kai wa shugaba Muhammadu Buhari hotunan irin gadan da yake son ya yi wanda ke da tsarin hawa uku. Ganduje na son Gina gadan ne a kan hanyar Kano zuwa Maiduguri, kuma ana sa ran za a sa wa hanyar sunan shugaba Muhammadu Buhari idan an kammala shi.

Kwankwaso ya gaya wa BBC Hausa ranar Juma'a cewa "Duk da yake muna bukatar gadan sama a shataletalen Kano, amma abin da jama'a suka fi so shi ne a ilmantar da yayansu, su samj sanaar yi domin dogaro da kansu".

"Marmakin Ganduje ya je ya nemi shugaba Buhari ya gina gadar domin aikin Gwamnatin Tarayya ne su gina gadar da zata hada Birnin Kano da Wudil amma sai ya gabatar da hotuna marasa inganci wanda shugaban kasa ya kasa ganewa domin akwai ayyuka da yawa a gabanshi" Inji Kwankwaso.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN