Kebbi: Yan bindiga sun farmaki Mussuru a Danko-Wasagu, sun sace matar aure cikin dare


Yan bindiga cikin duhun dare ranar Lahadi, sun farmaki kauyen Mussuru da ke Mazabar Dan Umaru a karamar hukumar Danko-Wasagu da ke Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi.

Yan bindigan sun shiga kauyen ne da misalin karfe daya na dare ranar Lahadi suka dinga barin wuta da bindiga, daga bisani suka dauke wata matar aure yar shekara 35 mai suna Mairi Alhaji Isiya.

Kawo yanzu dai babu Karin bayani kan irin barnar da harin na ranar Lahadi ya haifar. Sai dai mun samo cewa har yanzu Yan bindigan basu tuntubi iyalin matar da suka dauke ba.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Post a Comment

Please Select Embedded Mode To Show The Comment System.*

Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN