Jam'iyyar PDP Ta Dakatar Da Tsohon Gwamna Babangida Aliyu


Jam'iyyar PDP reshen jihar Niger ta dakatar da tsohon gwamnan jihar Niger, Dr Mu'azu Babangida Aliyu kan zarginsa da cin amanar jam'iyyar da hakan ya haifar da rabuwan kai a jam'iyyar tun 2014. Jaridar legit ta ruwaito.

Hakan na cikin sanarwar bayan taro da jam'iyyar ta fitar a karshen taron gaggawa na masu ruwa da tsaki da ta gudanar a garin Minna a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Sakon bayan taron da mutum 22 suka rattaba hannu a kai ya ce an dauki matakin kan tsohon gwamnan ne bayan shigar da korafi shida kansa wadda jam'iyyar a karamar hukumar Chanchanga ta lura abubuwan damuwa ne da ka iya hana jam'iyyar cigaba.

Kazalika, sakon bayan taron ya kuma bayyana cewa tsohon gwamnan ya yi aiki don ganin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da dan takarar gwamna a jihar Alhaji Umar Nasko sun fadi zabe ta hanyar taimakawa jam'iyyar adawa ta APC a 2015 da kudi Naira miliyan 450 don ganin jam'iyyarsa ta sha kaye.

Sakon bayan taron da aka raba wa manema labarai a jihar ta kuma ce zargin da ake masa sun hada da 'raba kan yan jam'iyya duk da tarurukan sulhu da aka yi'.

Har wa yau, laifukan da ake zarginsa da shi sun hada da rashin hallartar taron jam'iyya da wasu ayyuka wanda hakan ya janyo rabuwar kai da rashin samun nasarar cimma manufofin jam'iyyar.

Jam'iyyar ta ce, "wannan da wasu zargin da dama suka sa aka dakatar da Dr Mu'azu Babanigida Aliyu daga jam'iyyar Peoples Democratic Party a karamar hukumar Chanchaga ”.

Shugabannin jam'iyyar takwas cikin gundumomi 11 ne suka samu hallarton taron.

An yi kokarin ji ta bakin tsohon gwamnan amma bai daga wayarsa ba kuma bai amsa sakonnin kar ta kwana ba a lokacin hada wannan rahoton


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN