Hukumar gyara hali na kasar Afrika ta kudu ta tsunduma cikin abin kunya bayan an kama daya daga cikin ma'aikaciyar hukumar turmi tabarya tana lalata tare da wani dan kaso a yankin KwaZulu-Natal.
Wani faifen bidiyo da ya yi ta yawatawa kamar wutan dare ya tayar da kura a kasar ta Afrika ta kudu, lamari da ya jawo hankalin mahukunta a kasar.
Bidiyon ya nuna yadda ma'aikaciyar gidan gyara halinka sanye da damarar aiki, ta dinga sunbace tare da rungumayya da wani dan kaso a cikin wani daki Mai kama da ofis a cikin Kurkuku, lamari da ya kai su ga aikata lalata.
Kakakin hukumar gyara hali na kasar Afrika ta kudu Singabakho Nxumalo ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma tabbatar da cewa an dauki matakin ladabtarwa kan ma'aikaciyar tare da dan kaso da suka aikata lalata.
https://chat.whatsapp.com/Cw2uhGNZiIzGM88PV4gpOI
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari