Yansanda 2 sun mutu sakamakon rikicin kabilanci a jihar Taraba

An hallaka jami’an ’yan sanda biyu a sabon rikicin kabilanci tsakanin al’ummar Tibi da Jukun a Jihar Taraba.

’Yan sandan sun rasu ne yayin da wasu suka samu raunukan bindiga a harin da ’yan sa kai suka kai da sanyin safiyar Laraba a garin Chanchangi na Karamar Hukumar Takum ta Jihar Taraba.

Wani mazaunin Chanchangi ya ce shaida wa Aminiya cewa mahara dauke da muggan makamai daga Jihar Binuwai sun far wa garin ne suna harbi kan mai uwa da wabi, inda suka kashe ’yan sandan kwantar da tarzoma biyu suka raunata wasu da dama ciki har da kananan yara.Y

Yace yayin da harin ya jefa ’yan garin cikin firgici, mutane da dama musamman mata da kananan yara sun tsere, yayin da wasu maza suka yi dauki ba dadi da su da maharan.

Mutumin ya ce da zuwan maharan sai suka wuce zuwa fadar wani basarake za su shiga amma mutanen garin suka ja daga suka hana su, wanda a artabun ne aka jikkata wasunsu.

Ya ce daga baya an turo ’yan sanda garin suka fatattaki maharan, yayin da wasu mazauna ’yan kabilar Tibi suka tsallaka suka koma Jihar Binuwai.

Wata majiya a garin Takum ta ce an kai wasu daga cikin wadanda aka raunata Babban Asibitin Takum inda ake jinyar su.

A kusa da garin Chanchangi ne ’yan ta’adda suka yi garkuwa da matasan Takum 26 mako biyu da suka gabata.

Harin da ake zargin yaran tsohon dan ta’addan Jihar Binuwai, Gana ne suka kai, ya dawo da zaman doya da manja tsakanin ’yan kabilar Tibi da makwabatansu Jukunawa a Jihar Taraba.

Kakakin ’yan sandan Jihar, ASP Leha Refrom ya tabbatar ta da aukuwar harin da kuma kashe dan sanda daya tare da jikkata kananan yara hudu.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN