Yan bindiga sun yi awon gaba da babban Malami sheikh Muhammad Adam Rigachikun


Yan bindiga sun yi awon gaba da babban Limamin Masallacin Rigachikun a jihar Kaduna Shaikh Muhammad Saminu Adam, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa daurin aure a jihar Niger.

Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa an kama Malamin ne tare da sauran matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, da yammacin ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu.

Rahotun Jaridar ya ce Malamin yana cikin motar haya ne tare da sauran fasinjoji kafin yan bindiga su farmaki motar.

Sakataren Majalisar Ulama na jihar Kaduna Ustaz Yusuf Al’rigassiyu,  ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai wani mutum da baya son a ambaci sunansa ya ce yan bindigan sun tuntubi iyalin Malamin a wayar salula, amma ba karin bayani ko yan bindigan sun bukaci kudin fansa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN