Yadda ƙimar shugabar da ta goyi bayan yi wa Musulmai kisan kiyashi a Myanmar ta zube

Da sanyin safiya ne sojojin Myanmar suka tsare shugabar ƙasar Aung San Suu Kyi da sauran ƴan siyasa kafin ƙwace ƙarfin ikon ƙasar.

Juyin mulkin na zuwa ne bayan rikici ya barke tsakanin gwamnatin Suu Kyi ta farar hula da rundunar soji bayan zaɓe mai cike da ruɗani.

A zaɓen da aka gudanar a watan Nuwambar da ta wuce, jam'iyyar Suu Kyi ta National League for Democracy (NLD) ta ci yawan ƙuri'un da ya kamata a samu a kafa gwamnati.

Ranar Litinin, daf da lokacin da za a yi zaman majalisa na farko, rundunar sojin ta ce za ta miƙa mulki ga shugaban dakarun ƙasar Min Aung Hlaing saboda "maguɗin zaɓe".

Kafar watsa labarai ta soji ta ce ta sanya dokar ta-ɓaci tsawon shekara guda kuma ta miƙa mulki. Aung San Suu Kyi ta buƙaci magoya bayanta da "kada su amince da wannan" kuma su "yi fatali da juyin mulkin".

Myanmar, wadda ake kira Burma, ta fuskanci mulkin soja har sai da aka kawo sauye-sauyen dimokuraɗiyya a 2011.

A 2015, lokacin da aka gudanar da zaɓen farko ƙarƙashin tsarin dimokuraɗiyya, Aung San Suu Kyi ta ci zaɓe da wagegen giɓi.

Ana mata kallon wata babbar jigon dimokuraɗiyya da ta haƙura da ƴacinta don ta ƙalubalanci manyan sojoji marasa imani.

Haka kuma, ta ci gaba da samun goyon bayan al'ummar ƙasarta da mafi yawansu mabiya addini Buddha ne.

Amma ga sauran ƙasashen duniya, yadda ta tafi da rikicin Rohingya ya yi sanadiyyar zubewar ƙimarta, abin da mutane da yawa ba su yi zato ba.

Yadda ta hau mulki

Aung San Suu Kyi ta kwashe kusan shekara 15 a tsare tsakanin 1989 zuwa 2010.

A 1991, an ba ta lambar yabo ta Nobel Prize yayin da take tsare a gida kuma an yabe ta a matsayin "mai jajircewa duk da rashin ƙarfin ikonta".

US President Barack Obama meets Myanmar's Aung San Suu Kyi in the Oval Office of the White House, September 19, 2012
Bayanan hoto,

Gwamnatin Obama ta cire takunkumin da ke kan Myanmar bayan da suka koma Dimokuraɗiyya

Gwagwarmayarta ta kawo dimokuraɗiyya mulkin soja na wancan lokaci a Myanmar ya sa ta zama wata alama ta son zaman lafiya duk da zaluncin da ke gudana a ƙasar.

A watan Nuwambar 2015 ne ta jagoranci jam'iyyar NKD ta yi nasara a zaɓen dimokuraɗiyya na farko cikin shekara 25.

Kundin tsarin mulkin Myanmar ya haramta mata zama shugaba saboda tana da ƴaƴa da ba ƴan ƙasar ba.

Amma duk da haka ana yi wa Suu Kyi, mai shekara 75 a yanzu kallon shugabar ƙasar mai cikakken iko.

A hukumance ana kiranta 'state counsellor" wato mai bai wa gwamnati shawara. Shugaban ƙasar, Win Myint, na hannun damanta ne.

'Dole ne damu kan harkokin Myanmar'

Suu Kyi ƴa ce ga jagoran neman yancin Myanmar, Janar Aung San.

An kashe shi a lokacin da take da shekaru biyu, daf da samun ƴancin Myanmar daga mulkin mallakar Birtaniya a 1948.

A 1960, ta je Indiya tare da mahaifiyarta Daw Khin Kyi wadda aka naɗa jakadiyar Myanmar a Delhi.

Bayan shekaru huɗu ta tafi jami'ar Oxford da ke Burtaniya inda ta karanci Falsafa da Siyasa da Tattalin Arziƙi. A nan ne ta haɗu da mijinta malamin jami'a Michael Aris.

Bayan zama da aiki a Japan da Bhutan, ta natsu ta zauna a Burtaniya don rainon ƴaƴanta biyu, Alexander da Kim, amma ba ta taɓa mantawa da Myanmar ba.

Aung San Suu Kyi and Michael Aris with their first-born son Alexander Aris, London, 1973
Bayanan hoto,

Aung San Suu Kyi da Michael Aris da ɗansu Alexander a Landan a 1973

A lokacin da ta koma Rangoon (wanda yanzu ake kira Yangon) a shekarar 1988 - don yin jinyar mahaifiyarta da ke kwance rai a hannun Allah - Myanmar na tsaka da tashe-tashen hankulan siyasa.

Dubban ɗalibai da ma'aikatan gwamnati da malaman addinai na tattaki a tituna suna neman sauyi.

"A matsayina na ƴar mahaifina, ba zan iya ɗauke kai daga abubuwan da ke faruwa ba," ta ce a wani jawabi da ta yi ranar 26 ga Agusta 1988.

Ta jagoranci zanga-zangar nuna ƙin jinin shugaban wancan lokacin mai mulkin kama-karya, Janar Ne Win.

Tsare ta a gida

Ganin yadda aka gudanar da kamfe-kamfe cikin kwanciyar hankali, na shugaban ƙwato haƙƙin dan Adam, Martin Luther King na Amurka da Mahatma Ghandi na India, ta shirya zanga-zangar lumana tana yawo a faɗin ƙasar tana kira da a yi garanbawul a dimokuraɗiyyar ƙasar sannan a gudanar da sahihin zaɓe.

Amma sojoji a ƙasar sunhana zanga-zangar, kuma suka ƙwace mukki ran 18 ga watan Satumbar 1988. A shekarar da ta biyo baya aka tsare ta a gida ba a gidan kaso ba.

Gwamnatin soja ta shirya zaɓe a watan Mayun 1990, wanda jam'iyyar Suu Kyi ta NLD ta yi nasara - amma sojoji suka ƙi miƙa mulki.

Suu Kyi ta ci gaba da kasancewa a tsare a gida a Rangoon tsawon shekarar shidda, kafin a sake ta a watan Yulin 1995.

An sake tsare ta a gida a Satumbar 2000, lokacin da ta yi ƙoƙarin zuwa garin Mandalay duk da dokar taƙaita zirga-zirga da aka sa mata.

An sake ta a watan Mayun 2002, amma ba a dade ba aka sake ɗaure ta bayan karawa tsakanin magoya bayanta da wasu gun-gun magoya bayan gwamnati.

Aung San Suu Kyi greets supporters on her release from house arrest in 2010
Bayanan hoto,

Mutane da yawa ne suka tarbi Aung San Suu Kyi lokacin da aka sake ta a 2010

Daga baya an bar ta takoma gida - amma dai tana tsare a gidan.

A wasu lokuta, ta kan samu damar ganawa da sauran jami'an jam'iyyarta ta NLD da wasu jakadan ƙasashen waje, amma a shekarun farko-farkon ba ta ganin kowa kuma babu mai ganinta.

Ba a bari ta ga ƴaƴnta biyu ko mijinta wanda ya rasu a watan Maris din 1999 bayan fama da cutar daji.

Hukumomin soji sun ba ta damar tafiya Burtaniya don ta gano mijinta a lokacin da yake ciwon ajali, amma ta ƙi amincewa saboda fargabar za su hana ta dawowa ƙasarta.

Sake shiga harkokin siyasa

An hana Suu Kyi shiga zaben da aka gudanar karon farko na Myanmar cikin shekara 20 na ranar 7 ga watan Nuwambar 2010 amma an sake ta daga daurin talala kwana shida bayan hakan. An kyale danta Kim ya ziyarce ta a karon farko cikin shekaru da dama.

A yayin da sabuwar gwamnati ta soma gudanar da sauye-sauye, Suu Kyi da jam'iyyarta sun sake shiga harkokin siyasa.

Sun yi nasarar lashe kujeru 43 cikin kujeru 45 da aka yi takara a kansu a zaben cike gurbi da aka yi a watan Afrilun 2012, a wani mataki na nuna goyon baya karara a gare ta. An rantsar da Suu Kyi a matsayin 'yar majalisa kuma shugabar 'yan hamayya.

A watan Mayun da ya biyo bayan, ta bar Myanmar a karon farko cikin shekaru 24, a wata nuna kwarin gwiwar cewa shugabannin kasar za su bar ta ta koma.

Booklets bearing Aung San Suu Kyi's face in Myanmar after her party swept to victory in November 2015's election
Bayanan hoto,

Jam'iyyar NLD ta yi nasara a zabukan watan Nuwambar 2015

Rikicin Musulman Rohingya

Tun da ta zama jagorar Myanmar, an rika auna salon jagorancinta bisa yadda take tafiyar da lamuran Musulman Rohingya marasa rinjaye.

A shekarar 2017 dubban daruruwan 'yan kabilar Rohingya fsun tsere daga kasar zuwa makwabciyarta Bangladesh saboda dirar mikiyar da sojoji suka rika yi musu bayan an kai hari a ofisoshin 'yan sandan da ke jihar Rakhine.

Yanzu Myanmar na fuskantar shari'a inda ake zarginta da kisan kiyashi a Kotun Duniya, yayin da Kotun Hukunta masu aikata laifuka ta Duniya take gudanar da bincike kan kasar bisa aikata laifukan da suka dangancin cin zarafin dan adam.

Kasashen duniya da a baya suka goyi bayan Suu Kyi sun zarge ta da kin tsawatarwa yayin da sojoji suke yi wa mata fyade, da kisa da kuma kisan kiyashi.

Da farko mutane kalilan sun yi ikirarin cewa ita 'yar siyasa ce mai sassaucin ra'ayi, wadda ke kokarin shugabantar al'umma mai kabilu da addinai daban-daban masu sarkakiya.

Sai dai an kalli kariyar da ta fito ta nuna kan sojojin a wani lokacin jin ba'asi da Kotun Duniya ta yi a shekarar da ta wuce a Hague a matsayin wani yanayi da ya zubar da kimarta a idanun duniya.

Sai dai a kasarta, "the Lady", kamar yadda ake kiran Suu Kyi, tana da matukar farin jin a tsakanin mabiya addinin Buddha wadanda su ne suke da rinjiye kuma ba sa tausayin Musulman Rohingya.

Rahotun shafin BBCHausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN