Sirrin ƴaƴan kankana da ɓawonta ga ma’aurata


Kankana na ɗaya daga cikin kayan gona na marmari da ke da matukar amfani ga bil'adama.

Kankana wata aba ce mai dauke da ruwa mai zaƙi kuma mai amfani matuka ga jikin bil'adama.

Masana sun bayyana Kankana da ƴaƴan itaciyar mai matukar amfani ga rayuwar bil'adama, don sindarai da ke cikinta na Vitamins da Minerals da Antioxidants da kuma Calories.

Kankana na da nau'ika biyar: akwai mai ƴaƴa da mara ƴaƴa, akwai mai kalar ruwan dorawa da dan karami kore da mai kama da lemun zaƙi.

Sai dai a galibin kasashen Afirka irin Najeriya koriyar kankana mai ƴaƴan itatuwa aka fi sani.

Kashi 92 cikin 100 na kankana ruwa ne zalla, don haka mai yawaita shanta ba shi da matsalar ƙarancin ruwa a jiki, musamman lokacin zafi, in ji Maijidda Badamasi Burji da ke da ƙwarewa a ilimin abinci mai gina jiki.

Ga wasu abubuwa 9 da ƙwararru ke cewa kankana na iya a jikin dan Adam:

Kara ruwa a jiki

Rashin shan ruwa na illa sosai ga jikin dan adam, hakan yasa ake yawaita jan hankali mutane kan alfannu shan ruwa domin inganta lafiyar jiki.

Sai dai shan ƴaƴan itatuwa irin kankana wanda kashi 92 cikin 100 ruwa ne zalla zai maye gurbi bukatar da ake da ita na yawaita shan ruwa.

Sannan kankana baya ga ruwa akwai sinadarin Fiber a jikinta, don haka shan ta tamkar anci abinci ne mai matukar inganci wanda ke kunshe da galibin sinadarin da jiki ke bukata.

Sinadarin Vitamins da Minerals

A cikin jeren kayan marmari ko itatuwa, Kankana ita ce wacce ke da karanci sinadarin calories.

Calories din da ke jikinta bai kai na ƴaƴan itatuwa da ake ganin kwata-kwata basu da zaki ba, danginsu inibi.

Kofi guda na ruwan kankana na kunshe da sinadaran Vitamin C da A da Potassium da Magnesium da Vitamis B1 da B5 da B6.

Kariya daga daji ko Cancer

kankana
Bayanan hoto,

Shanruwan kankana ma yana da amfani

Daga cikin sindaran da ake samu a jikin kankana akwai masu bada kariya daga wasu nau'ikan ciwon daji ko cancer.

Bincike ya nuna cewa masu yawaita shan kankana masu fiye kamuwa da cancer ciki ba.

Kariya daga ciwon zuciya

Ƙwararu sun sha cewa ciwon zuciya shi ne kan gaba wajen hallaka mutane a duniya baki ɗaya.

Sai dai an lura akwai nau'in cimakar da ke taƙaita bugun zuciya da shanyewar barin jiki ta hanyar rage kamuwa da hawan-jini da rage kitse a jiki.

Sinadarai da dama a jikin kankana na iya samar da waraka da taimaka wajen yaƙi da wadanan cututtuka.

Garkuwa da kuzari

Kankana na bai wa jiki garkuwa, sannan yana taimakawa da sinadarin da ke taimawa halittar da suke yaki da cututtuka da kuma samun wakara daga ciwo ko rauni, sannan tana maganin kasala da sa kuzari

Ƙwarin Ido

Shan kankana na kara ƙwarin ido da kariya daga kamuwa daga wasu cutuka ido masu lahani ko kai wa ga makanta.

Mutanen da ke yawaita shan kankana ko ɗiga ruwanta a ido kan tsufa da idanunsu a cewar ƙwararu

Kumburin gabobi

Sinadarin citrulline, da ke jikin kankana, na rage kumburin gabobi. Sannan ana amfani da shi a hada magunguna kara ƙwarin gabobi da cutukan da ake samu saboda yawaita zama ko kin motsa jiki.

Hakazalika yawaita shan kankana da bada kariya daga kamuwa da Basir.

Gyara fata da gashi

Vitamins A da C na cikin kankana na da muhimmanci sosai wajen baiwa jiki sinadarin collagen da ke sa fata laushi da kyau da gyara gashi da kwari

Taimaka wa wajen narkewar abinci

Kankana da kunshe da ruwa sosai don haka shanta na taimaka wajen narkewar abinci.

Yawaita shanta na hana cushewar ciki da bai wa jiki dama sarafa abinci da narkewarta cikin dan kankanin lokaci.

Ko ku san sirrin ƴaƴan kankana?

Watakil kana/kina cikin mutanen da ke zub da ƴaƴan kankana wajen shanta - ko tsameta kafin ayi amfani ko sarafa kankana.

To ga wasu bayanai masu muhimmanci da muka tattara da ka iya taimaka mu ku wajen sauya ra'ayi kan ƴaƴan kankana a tattaunawarmu da Maijidda Yahaya.

Ƴaƴan kankana na da sirika sosai da ba kowa ya san da su ba, suna kunshe da sinadarin Zinc da Magnesium da Potassium da Iron da dai sauransu.

Ƴaƴan kankana na bai wa jiki garkuwa da matsalar ciwon zuciya da hana ko warkar da ciwon suga da inganta jima'i.

Ga karin alfannunsa ga jikin dan adam

1. Yana sa kuzari

2. Inganta jima'i ko saduwa

3. Gyara maniyin maza musamman masu matsalar haihuwa

4. Inganta lafiyar kwakwalwa

5. Kwarin kashi

6. Garkuwar jiki

7. Warkar da Ciwon suga nau'i na biyu ko Diabtes type 2 a Turance

8. Ƴaƴan kankana na gyara gashi ga mace

9. Gyara fatar jiki

10. Lafiyar zuciya

Yadda ake sarafa ƴaƴan kankana

Kana iya taunewa hade da kankana, ko a shanyata ta bushe ko a soyata sama sama. Duk yada mutum ya sarafata zai ji dadinta.

Ɓawon kankana -Boyayyar sirri da akasari ba a san da shi ba

Na san galibin mutane idan ana shan kankana zub da ɓawonta ake yi ko a shanye jiki a ɓare bayan a zubar.

To kamar dai ƴar'uwarta gurji, ita ma kankana kyanta a shanye komai har da ɓawonta da galibin lokuta ake ganin an watsar a cikin shara, a cewar ƙwararu.

Ga wasu dalilai da ka iya sa ki/ka gamsu da waɗanan bayanan

1.Tana kara gamsuwa wajen kwanciya.

To amma fa kankana ba maganin karin kuzari ba ce, sai dai wani bincike ya nuna cewa za ta iya taimakawa maza wajen magance matsalar saurin kawowa. Tasirinta wajen kara karfin maza yana zuwa ne daga sinadarin amino da ke jikin ɓawonta.

Wani binciken ya nuna cewa sinadarin L-citrulline da ke cikin kankana zai iya taimakawa wajen inganta yanayin karfin maza ba tare da wasu illoli da ake samu a magungunan karfin maza ba.

Hazalika ga mata ɓawan kankana na taimaka musu wajen karin ni'ima musamman idan aka markadata cikin madara, in ji Maijidda Yahaya kwarariya kan abinci masu gina jiki.

2. Inganta maka kuzari

Za kuma ta iya inganta maka kuzari bayan kara nishadi a gado, domin sinadarin ruwan citrulline zai iya taimakawa wajen kara kuzari yayin motsa jiki.

3. Maganin hawan jini

Idan likita ya ce akwai bukatar jininki ya yi kasa, to gwada cin kankana baki dayanta - har da ɓawonta.

Binciken masana ya nuna cewa shan kankana na taimakawa manya da tsoffi musamman masu ƙiba yin maganin hawan jini.

Wata dabarar jin dadin kankana kamar yadda ƙwararru a fanin abinci mai gina jiki ke cewa, shi ne a sanyata a firij don ta yi sanyi a yankata sala-sala a shanye baki daya.

4. Tana kunshe da Sinadarin Fiber

Wani alfannun kankana ga jiki shi ne tana ƙunshe da sinadarin Fiber sosai da ke taimakawa matuka wajen kariya daga cututuka, rage kitsen jiki ko suga, da kuma cimma buri ga masu son rage kiba.

Karin haske

Wani karin haske da shawarwarin ƙwararru kan shan kankana shi ne mutum na iya bare ɓawonta ya yanka sala-sala sannan ya barbade da yaji, ma'ana a yi kwadonta ga wadanda cin ɓawon zai yi wa wahala.

Rahotun BBCHausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN