Ko da gaske ne shugabannin Majalisar Tarayya za su goyi bayan a ba Ibo sabuwar Jiha ?


Tsohon shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, John Nwodo, ya jagoranci tawaga zuwa majalisar tarayya, su na neman a kirkiro masu sabuwar jiha, Jaridar legit hausa ta ruwaito.

The Cable ta ce Cif John Nwodo da mutanensa su na so a fito da wata jiha da za a kira jihar Adada, daga cikin bangaren Enugu a yankin Kudu maso yamma.

Jaridar ta ce wannan tawaga ta kai ziyara zuwa majalisar tarayyar ne a ranar Laraba, 9 ga watan Fubrairu, 2021, inda su ka gana da shugabannin majalisar.

John Nwodo ya zauna da shugaban majaliar dattawa, Ahmad Lawan, da mataimakinsa, Ovie Omo-Agege, da kuma Femi Gbajabiamila, da Idris Wase.

Ya ce fafutukar neman jihar Adada ta fita dabam saboda babu wanda yake adawa da neman jihar a Enugu ko a wajen jihar, kuma duk Ibo sun karbi maganar.

Idan an yi na’am da wannan jiha, zai zama akwai jihohi uku ta bangaren Arewacin kasar Inyamurai kamar yadda ake da jihohi uku daga shiyyar Kudu.

A ganawar da aka yi da shugabannin majalisar a lokuta dabam-dabam, an shaida wa Nwodo cewa babu wanda yake adawa da wannan jiha da su ke nema.

Lawan ya yi na’am da bukatar da masu fafutukar su ke yi, ya ce majalisa za ta saurari kukansu.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Omo-Agege ya yi maraba da wannan yunkuri, ce za su duba maganar kirkiro wannan sabuwar jiha ta Adada.

A baya mun kawo maku rahoto cewa tsohon shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta mutanen Ibo, John Nnia Nwodo, ya koka a kan nadin hafsun sojojin kasa.

Cif John Nnia Nwodo, ya yi tir da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari na ware mutanen kasar Ibo a mukaman da ya bada a gidan sojan Najeriya.

Ita ma kungiyar Afenifere ta ce nadin da aka yi jiya ya sake nuna son kan Muhammadu Buhari.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN