Hadimin Buhari ya magantu kan zancen nada sàbon shugaban yansanda


Shafin labarai na legit ya rewaito cewa shiru ake ji dangane da batun zaben sabon Sifeta janar na 'yan sanda sakamakon karewar wa'adin IGP Mohammed Adamu a ranar Litinin.

Fadar shugaban kasa bata sanar da wani tsayayyen lokaci ba na sanar da wanda zai gaji kujerarsa ba, The Nation ta wallafa.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, a ranar Litinin da ana tattaunawa da shi a gidan talabijin din Channels ya ce bai san komai ba dangane da al'amarin.

Shehu ya ce ya san dai idan za a sake zaben sabon IGP, cancanta za a duba ba wai bangaranci ba.


"Shugaban kasa zai koma Abuja a ranar Talata. Kuma zai koma bakin aikinsa a ranar Laraba. Ban san lokacin da zai yi magana ba akan wannan al'amarin.

"Abinda zan tabbatar muku shine, Shugaba Buhari zai gwammaci ya samar da sabon sifeta janar wanda zai kula da ni da kai ba wai ya duba kabilanci ba.

"Idan aka duba batun bangaranci kuwa za a iya zaben akalla sifeta janar guda 250, hafsoshin soji guda 250 da sauransu. Don haka ba mai yuwuwa bane," yace.

A wani labari na daban, asbbin hafsoshin tsaron kasar nan sun kai ziyararsu ta farko jihar Borno, jihar da ta kasance filin daga da 'yan Boko Haram.

Sun samu ganawa da Gwamna Zulum a Maiduguri, tsohon gwamnan jihar, Sanata Kashim Shettima ya samu halartar zaman.

Shugaban ma'aikatan tsaro, manjo Janar Leo Irabor ya jagoranci shugaban sojin tudu, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, shugaban sojin ruwa Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo da shugaban sojin sama, Air Vice Marshal isiaka Oladayo Amao zuwa gidan gwamnatin jihar.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN