Fani Kayode yana shirin komawa jam'iyyar APC


Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode zai yuwu yana kan hanyarsa ta komawa jam'iyya mai mulki ta APC bayan kwashe shekaru 6 da yayi da barin PDP, Jaridar legit hausa ta ruwaito.

Majiyoyi kusa da shi sun sanar da The Nation yadda ya samu ganawa da shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buuni tare da takwaransa na jihar Kogi, Yahaya Bello a Abuja.

Ganawar sirrin wacce ta dauka tsawon sa'a daya, an gano cewa tana da alaka da shirin komawar tsohon ministan jam'iyyar APC.

Tun kafin nan, Fani-Kayode ya gana da Gwamna Bello a gidansa da ke Wuse Zone 6 a Abuja kafin su garzaya zuwa gidan saukar bakin Gwamna Mai Mala Buni.

A wani labari na daban, kotun jihar Legas ta laifuka na musamman dake Ikeja ta yanke wa faston Living Faith Church wacce aka fi sani da Winner's Chapel, Afolabi Samuel, shekaru 3 a gidan gyaran hali bisa satar $90,000 da N4,500,000 wanda 'yan coci suka hada karfi da karfe suka tara.

EFCC ta gabatar da Samuel wanda shine akawu kuma ma'ajin cocin gaban alkali Mojisola Dada bisa laifuka biyu, almundahana da sata.

Kamar yadda EFCC ta gabatar, faston da wata Blessing Kolawole, wacce take aiki a jami'ar Covenant, sun hada kulle-kullen satar dukiyar kuma sun sake a aljihunansu don amfaninsu.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN