Duba dalili da ya sa Kotu ta kori karar da Sheikh Abduljabbar ya shigar kan Gwamnatin jihar Kano


Babbar Kotun Tarayya a Najeriya da ke zamanta a Kano ta kori ƙarar da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya shigar gabanta yana neman ta umarci gwamantin Kano ta cire ɗurin talalar da take yi masa.

Mai Shari'a Lewis Alagoa ya kori ƙarar ce bayan lauyan Abduljabbar, Rabi'u Shu'aibu Abdullahi, ya gabatar da buƙatar mai ƙarar ta janye ƙorafin nasu daga gaban kotun.

Lauyoyin da ke kare gwamnati ba su yi wata-wata ba suka amince da buƙatar kuma nan take mai shari'a ya kore ta.

A ranar Alhamis da ta gabata ne shehin malamin ya shigar da ƙarar da zummar neman kotu ta tilasta wa gwamnati da kwamishinan 'yan sanda da shugaban tsaro na hukumar DSS a Kano da su janye jami'an su da suka girke a kofar makarantarsa da gidansa a unguwar Filin Mushe.

Gwamnatin Kano na tsare da malamin ne a gidansa biyo bayan zarginsa da "kalaman tayar da fitina" game da lamuran Musulunci a farkon watan Fabarairu.

Malamin ya musanta zargin sannan ya buƙaci a haɗa muƙabala tsakaninsa da sauran malamai a jihar, buƙatar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya amince kuma ya ce gwamnati za ta saka rana da wurin da za a gudanar da ita.

Rahotun BBCHausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN