Duba amfanin Kanumfari a jikin mutum


Sunan Kanumfari ya samo asali ne daga wata kalmar Larabci, wato ‘Karanful’, yayin da kuma da Turanci ana kiran sa da suna ‘Cloves’ ne. Ana noma shi ne galibi a tsuburai ne, mu dai nan nahiyar Afirka, akan same shi ne a tsuburin Pemba da Zanzibar na kasar Tanzaniya. Kusan Kanumfarin da wadannan tsiburan suke fitarwa ya ishi nahiyar tamu ta Afirka gaba daya, a kasar Indonesiya aka san shi, ko ma a ce kasarsa ke nan ta asali, akan yi aiki da shi  ne don abicin da ake sa wa sukari kamar Fura, Kunu, Buredi, Nakiya da dai sauransu, akan kuma sa a duk abincin gishiri don kara kanshin shi abincin ne.

Kanumfari ya kunshi abubuwa ko sinadarai masu yawa dangane da lafiyar jikin dan adam, kamar su Vitamin A, C, K, Iron, Calcium, Potassium, Magnesium, Phosphor, Sodium, Manganese, yana da Calories 21, Fats 1.32, Saturated fats 0.35, Carbohydrates 4.04, Fibres 2.3, Proteins 0.39, Cholesterol 0, wannan yana nuna kenan ashe Kanumfari fari zai iya zama babban abin da mutum zai bukata don rayuwarsa ba ma wai don yana sa  kanshin abinci ko ba, ko abin.

1) Bari mu fara da mai ciki, ko kuma a kira da suna mai juna biyu, wacce take bukatar ta sanya Kanumfari kadan don kara kamshin girki, (ya dace a lura nan, saboda ai an ce kadan  ne a nan domin idan ya yi yawa zai iya yin illa, in da hali za a iya yin bayanin yadda yake da mummunar illa ga mai ciki) zai taimaka wajen kara lafiya gare ta da jaririn nata, domin shi Kanumfari ya kunshi sinadarin Iron wanda duk wata mai ciki take bukata, ko don kara mata lafiyarta da ta jaririn da take dauke da shi.

Ba shi kadai ba ma, tana bukatar sinadaran Phosphor, Sodium, Manganese domin samun girman jaririn, mace tana bukatar VitaminC wanda zai taimaka mata wajen karfafa garkuwar jikinta, sananne ne duk wata mai ciki garkuwarta ta kan ragu sosai a dalilin shi cikin, shi Kanumfari yana da Antiodidants, ke nan wannan ya nuna zai iya taimakawa don ba wa mai juna biyu kariya, a lokacin da take da da cikin, masamman ma ta yadda yake da Fibres din da zai iya taimaka mata ko ya ba ta  wata kariya daga rikicewar ciki, Kanumfari yana da Omega- 3 fatty acids wanda yake taimakawa jijiyoyin jikin jaririn.

Kamar yadda aka yi bayani ne a baya cewar, ya kunshi sinadarin Calcium da Phosphor, wadannan su biyu su kan taimaki kasusuwan jaririn ne yadda za su yi karfi, hattanama in sun girma ma, kamar karfin hakoransu, in wata mai juna biyun tana so za ta iya sanya kadan matuka a abinci, ko ta yi kamar ado da shi a Buredi, a Cincin da dai sauransu, kar a manta shawara da likita a nan yana da matukar amfani, zai iya ba da shawarar a yi amfani da shi gwargwadon da mai juna biyu take bukata, ko ma ya hana ta amfani da shi gaba daya, don tsoron kar ta barad da cikin, a nan in ciki ya isa haihuwa zai iya taimakawa a sami saurin haihuwa kamar Dabino ke nan, yadda yake da hadari amma idani aka ci  shi da yawa ga mai ciki, yake da amfani sosai ga wacce cikin ta ya isa haihuwa.

(2)  Dangane da fata kuwa, tabbas Kanumfarin ya kan taimaka wajen samun fata mai kyau, yana da Antiodidants wanda yake fito na fito ko kuma yaki da Free radical, wanda wani sinadari ne wanda yake cutar da fata sannu a hankali, wannan ya fi bayyana ne tare da karuwar shekaru, sai fata ta fara kaushi-kaushi ko ma ta fara tattarewa, ba ma tattarar kadai ba ce, hatta kurarrajin girma da suke feso wa akan yi aiki da Kanumfari don kawar da su, akwai bukatar ayi shawara da likita dangane da kanumfari.

Idan ya kasance kurarrajin girma suna damun mutum, akwai bukatar ya yi wani hadi don kawar da su, wato ya sami nikakken Kanumfari karamin cokali, zuma kamin cokali, ya dan diddiga lemon tsami ya kwaba, sai ya shafa a fuskar, ya bar shi na dan wasu ‘yan mintuna kamar ashirin haka, sai ya wanke da ruwan dumi, a shekara ta 2009 ne wasu Sinawa suka gudanar da wata jarabawa akan man Kanumfari, don sanin tasirinsa wajen maganin Bacteria ko kwayar cutar da take haifar da kurarrajin girma, a karshe sun gano cewa man Tafarnuwa yana da tasiri mai girman gaske wajen cin galabar wannan Bacteria din.

(3) Kanumfari yana da babbar rawar da yake takawa dangane da magance matsalar Hakori, da warin numfashi, dangane da shi warin numfashi wani lokaci ba rashin wanke  shi bakin ba ne, in mutum zai wanke baki da duk man Hakorin da ya sani, ba zai iya maganin ita wancan matsalar ba, idan har warin ya yi yawa yana tasowa ne daga ragowar abincin da aka ci to lokacin da aka zo goge Hakoran za a iya kawar da shi, an gama ke nan, amma idan yana da alaka da dasashi, ko makogwaro, wannan dole sai mutum ya ga likita.

Ana aiki da Kanumfari don kawar da matsalar radadin hakori, Kanumfari yana dauke da sinadarin Eugenol wanda yake taimakawa wajen kawar da radadin hakori da na dasashi, dama aikin wannan sinadari yakan kashe radadi ne, shi kuwa Hakori ba zai bar mutum ya sake ba, ka ga kanumfari zai yi daidai da wannan wurin, irin wannan yanayin sai mutum ya sanya kan kwayoyin Tafarnuwan daidai gwargwado a baki, ya rika tsotse su har sai sun yi taushi daganan sai ya tauna ya matsar inda yake radadin.

A nan yana da kyau ya fahimci cewa ba maganin cutar aka yi ba, kashe zafinta aka yi na wani lokaci, za kuma a iya sanya garinsa a inda yake damun mutum, sai dai kamar yadda muka fadi ne, sinadarin Eugenol ne yake wannan aikin, za a iya samun Poison a cikinsa, yana da kyau kar a yi aiki da Kanumfari ga kananan yara wai don ganin yana taimakon manya, zai yi kyau mu gane cewa wadannan hanyoyi ba sau daya kadai ake bi ba, sai an yi ta maimaitawa, shi ya sa muke gargadin cewa a ga likita dangane da Kanumfari, wanda ya je maganin Gyambon ciki, ko Tari, ko wata cuta in bai bi ka’ida ba yana iya karuwa, a haka za ka iske ba mu kira sunan likita kamar yadda muke kiraN Kanumfari ba.

(4) Sai maganar Tari da warin numfashi, wadannan abubuwa guda biyu za a iya kawar da su ta hanyar kanumfari, kasancewar warin numfashi ba wai ga Hakoran kawai suke tasowa ba, wanda in da a ce daganan ne da an tsaftace su hakoran, da mai shi kenan an gama, amma idan, har shi doyin dai bari ba, to sanya kanumfari a cikin abincin da muke ci yau da kullum, kawai zai taimaka a wannan bangaren, mansa kuwa zai iya taimakawa wajen kawar da manyan matsaloli kamar Tari, Mura, Asthma, cutar makogwaro masamman wajen shakar numfashi, da kumburi tare da radadin hanci.

Wata shahararriyar likita a Amurka ta yi tsokaci kan cutar Asthma, akan wasu bincike masu yawa da aka gudanar, inda take nuna cewa Kanumfari kan magance cututtuka masu yawa ta hanyar wani sinadari dake cikinsa wato Eugenol, kusan wannan Eugenol din shi ne Component ko kuma sinadarin mafi girma da za a iya samu a cikin Kanumfari, akan magance cutar Asthma ta hanyar yin amfani da wannan Kanumfari din, yadda suke yi kuwa shi ne:

Akan sami kwayoyin Kanumfarin ne da silin ganyen Raihan /ٖrai’haan/ wanda muka fi sani da “Lemon grass” guda 12 zuwa 15, sai a debii ‘yan kwayoyin masoro kamar guda goma haka a watsa su a ciki, sai a tafasa shi na kimanin minti 15, sai a dan tarfa ko sanya zuma kamar cokali biyu da madara ita ma kamar haka, sai a juya a sha, wannan za a rika maimata shansa na dan wani lokaci, yana da dadin sha, bayan haka  kuma  ga magani.

Rahotun Jaridar Leadership


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari 


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN