Ministan harkokin waje na jamhuriyar Benin da ke makwabtaka da Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya ce a shirye kasar Benin take domin kasancewa jiha ta 37 a kasar Najeriya.
Ya ce shugaban kasar jamhuriyar Benin ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari wannan tayi lokacin da ya ziyarce shi yan makonni da suka gabata a Abuja.
Ya ce shugaban kasar Benin ya ca "A hakikanin gaskiya, ba wai kawai a furta da baki ba kawai, amma a zahiri, kasar Benin ya kamata ta zama jiha ta 37 a kasar Najeriya.
Ya kamata mu zama daya, sun bukace mu a mataki na shugabanci mu fito da tsari da zai jaddada dankon zumunta a tsakanin mu.
Onyeama ya ce shugabannin kasashen biyu, sun tattauna tare da yarjejeniyar ganin kasashen sun kawo karshen fasa kwabri a iyakokinsu.
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari