Jaridar TheCable ta fahimci cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu yayin da gwamnan ke kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri.
Zulum na dawowa ne daga karamar hukumar Mafa (LGA) inda ya je sabonta rijistarsa na dann jam'iyyar All Progressives Congress (APC) lokacin da hatsarin ya faru
Wata majiyar ‘yan sanda da ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce wani basarake na daga cikin wadanda suka mutu
A cewar 'yan sandan, motar da ke dauke da Mai-Kanuribe, wani hakimin Borno da ke Legas, ta kife bayan da tayar ta fashe, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa da kuma wani fasinja guda daya.
An garzaya da mutane biyu da suka jikkata zuwa asibiti yayin da aka kai gawarwakin mutanen biyu da suka mutu zuwa Maiduguri.
Wannan lamarin ya zo ne watanni hudu bayan maharan Boko Haram sun kai wa ayarin motocin Zulum hari sau biyu a cikin mako guda.
A wani labari na daban, Fulani makiyayan dake kudu maso yamma, kudu maso gabas da wasu sassan Najeriya sun bayyana niyar komawa jihar Kano inda aka shirya musu shirin RUGA.
Sakataren kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), a jihar Kano, Zubairu Ibrahim, ya bayyana hakan.
A cewar Ibrahim, makiyayan sun hada wadanda ke zaune a jihar Nasarawa, Neja, Enugu, Oyo, da sauran su.
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari