Wasu mutane sun dauke wani basaraken garin Dega, rikon garin Tadurga, mai suna Dega Na'Allah, ranar Litinin 15 ga watan Fabrairu da misalin karfe 5 na yamma a karamar hukumar Zuru da ke Masarautar Zuru a kudancin jihar Kebbi.
Rahotanni sun ce ana zargin cewa wasu mutane dauke da makamai, sun tsayar da basaraken ne kuma suka saukar da shi daga babur da yake tukawa, lokacin da yake dauke da matarsa kan hanyarsa ta komawa gida, sun tsayar da shi a dai dai kofar barka da zuwa garin Ribah suka yi awon gaba da shi.
Tun ranar Litinin 15 ga watan Fabrairu, har zuwa yanzu, ba a ji duriyar inda yake ba tare da babur da yake tukawa.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/HUEzyk9QvHZ6kSk4bH2U6K
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari